Home Labarai Shugaba Mugabe na Zimbabwe ya bayyana a karon farko tun bayan da soji suka kwace iko a kasar

Shugaba Mugabe na Zimbabwe ya bayyana a karon farko tun bayan da soji suka kwace iko a kasar

0
Shugaba Mugabe na Zimbabwe ya bayyana a karon farko tun bayan da soji suka kwace iko a kasar

A yau Juma’a aka ga Shugaba Robert Mugabe na ZImbabwe a bikin saukar karatun daliban Jami’ah a babban birnin kasar Harare.

An ga Shugaba Mugabe sanya da kayan girmamawa na bikin saukar karatun daliban Jami’ah. Shugaban wanda ya shafe kusan shekaru 37 yana jan ragamar kasar ta Zimbabwe tun bayan samun mulkin kai daga kasar Birtaniya.

A farkon makon nan ne dai aka wayi gari sojoji sun karbe ikon tafiyar da kasar, yayin shugaba Mugabe yake samun kulawa a hannun jami’an tsaron sojan kasar.

Lamarin dai ya auku ne, bayan wani rudani da ya auku a kasar sakamakon sauke mataimakin shugaban kasar da Mugabe yayi, yake shirin maye gurbinsa da mai dakinsa Grace Mugabe.