Home Labarai Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin dawo da ‘yan Najeriya gida daga Libiya

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin dawo da ‘yan Najeriya gida daga Libiya

0
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin dawo da ‘yan Najeriya gida daga Libiya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin mayar da dukkan ‘yan najeriya da suke a kasar Libiya da ma sauran ‘yan Najeriya dake halin galabaita a kasashen duniya.

Shugaban ya bayar da umarnin ne daga birnin Abidjan na kasar Kwadebuwa, a wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban kasa ya fitar a ranar laraba.

Shugaba Buhari ya yi jawabin ne a lokacin da yake tattaunawa da kungiyar ‘yan Najeriya mazauna kasar ta Kwadebuwa, a babban birnin wato Abidjan, inda yake halartar wani muhimmin taro.

Shugaba Buhari ya sha alwashin rage yawan adadin ‘yan najeriya dake yunkurin tudada zuwa kasashen Turai ta kowacce hanya. Musamman hanyoyi masu hadari da suka hada da Hamadar Sahara da kuma Tekun meditereniya.

Samar da abubuwan more rayuwa da suka hada da Ilimi da lafiya da inganta aikin noma wanda zai baiwa dubban jama’a aikinyi da kuma samar da abinci ga dumbin al’ummar Najeriya, a cewar Garba Shehu.

Duk wasu hanyoyi da suka dace ana kokarin binsu domin ganin an dakile kwarar ‘yan Najeriya zuwa kasashen Turai ta barauniyar hanya domin neman ingantacciyar rayuwa a can kasashen Turai din.

Abu ne mai wahalar gaske, a iya gano ainihin garuruwan mutanan da suka mutu a yunkurinsu na tafiya kasashen Turai a kasar Libiya da tekun Meditereniya, kasancewar duk masu tafiyar babu wasu cikakkun bayanai da suke nuna inda suka fito.

“Lokacin da aka bayar da sanarwar, mutuwar mutum 26 ‘yan Najeriya a tekun Meditereniya, kafin a tabbatar da cewar mutanan ‘yan Najeriya ne ko ba ‘yan Najeriya bane, tuni aka binne su a wajen”

“Amma a bisa bayanan da na samu daga mai bani shawara kan ‘yan Najeriya dake zaune a kasashen waje, mutum uku daga cikin ashin da shidan da aka ce ‘yan najeriya ne suka mutu, uku ne kacal bayanai suka tabbatar da cewar ‘yan Najeriya ne”

“Amma ba zan yi mamaki ba, idana aka ce dukkan mutanan ‘yan Najeriya ne. Mutanan su dinga yin wannan tafiya mai cike da hadai suna hawa kwale kwale a cikin teku, zamu yi abin da zamu iya wajen ganin mutanan sun zauna a gida Najeriya”

“Duk wani mutum da zai mutu a cikin sahara ko a tekun Meditereniya, matukar babu wasu cikakkun bayanai da suka nuna cewar dan Najeriya ne, to babu wani abu da zamu iya yi a gwamnatance domin babu hanyar da zamu gane namu ne”

“Abin takaici ne da kaduwa kwarai da gaske, muga hoton bidiyon da ake sayar da ‘yan Najeriya kamar awaki a matsayin bayin da aka yi garkuwa da su, akan kudin da bai taka kara ya karya ba, a kasar Libiya”

Shugaba kuma, ya tabbatar da ‘yan najeriya dake zaune a kasar ta Kwadebuwa cewar, akwai abubuwa masu dadi dangane da Najeriya, domin ana samun ingantuwar tsaro da sha’anin tattalin arziki da aikin gona da sauran.