Home Labarai Gwamna Ganduje ya bukaci Kwankwaso ya nemi afuwar Buhari ko ya fuskanci mataki mai tsauri

Gwamna Ganduje ya bukaci Kwankwaso ya nemi afuwar Buhari ko ya fuskanci mataki mai tsauri

0
Gwamna Ganduje ya bukaci Kwankwaso ya nemi afuwar Buhari ko ya fuskanci mataki mai tsauri
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana rashin jin dadinsa akan kalaman tsohon Gwamnan jihar Rabiu Musa Kwankwaso, inda ya zargi Shugaba Buhari da hannu wajen cire Shugaban APC na jihar Haruna Doguwa.

A ranar lahadi da ta gabata ne, tsohon Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya zargi Shugaban kasa Muhammadu Buhari da hannu wajen cire Shugaban jam’iyyar APC na jihar, Haruna Douwa, wanda dan bangaren Kwankwason ne.

Alokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano ranar Asabar, Shugaban ma’aikatan Sanata Kwankwaso yace, Shugaba Buhari ne da kansa ya bayar da umarnin a cire Haruna Doguwa daga mukaminsa.

A ranar lahadi da ta gabata, Shugaba Buhari ya gargadi ‘yan Kwankwasiyya da su daina sanya sunansa kan batun rikicin siyasar Kano.

A wata sanarwa day a fitar ranar talata, Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Muhammad Garba, yace kalaman tsohon Gwamnan, cin zarafi ne da rashin mutuntawa ga Shugaba Muhammadu Buhari.

A dan haka ne, Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje, ta bukaci ‘yan kungiyar ta Kwankwasiyya das u nemi afuwar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, kuma su janye kalaman da suka yi akansa.

Idan basu yi haka ba kuma, zamu yi kira ga uwar jam’iyyar APC ta kasa da ta dauki mataki mai tsauri akansu, domin abinda suka yi din cin zarafi ne ga jagoranmu Shugaban kasarmu.

“Gwamnatin Kano tana mai jininawa ‘yan jam’iyya da suka kasance masu mutunci da da’a yayin wannan sabatta juyatta da kuma satoka sakatse da ake ta yi a cikin jam’iyyar, amma duk da haka suka cigaba da zama masu biyayya, wannan abin a yaba musu ne kwarai da gaske”

“Duk da ‘yan jam’iyya sun san yadda ‘yan Kwankwasiyya suka dinga yamutsa hazo, suna yin abubuwa na rashin gaskiya da kokarin tayar da zaune tsaye amma Allah bai basu nasara ba, suna yiwa jam’iyya karantsaye, muna yabawa ‘yan jam’iyya kan jajircewarsu”

“A yanzu da aka samu sabon Shugaban jam’iyya, wanda shi ne halastaccen shugaba wanda uwar jam’iyya ta kasa ta sanar, idan har ‘yan kwankwasiyya sun cika masu da’a ga wannan jam’iyya to su zo su yi masa biyayya, domin shi ne sahihin Shugaban APC na jihar Kano”