Home Labarai Mai Tatsine a shirin maza Gumbar Dutse

Mai Tatsine a shirin maza Gumbar Dutse

0
Mai Tatsine a shirin maza Gumbar Dutse

Shirin maza gumbar dutse wani shirine wanda Dattijon arziki kuma shahararren Malami me makarantar yaki da jahilci Alh Baban Ladi ke gabatarwa a gidan rediyon Rahama f.m. (97.3) Kano a duk ranar Laraba karfe 10 na dare zuwa 11.

Shirin yana daga cikin shirye-shiryen rediyo da suke kayatar dani kuma yanada dubban masu sauraro. A cikin shirin akan gayyaci wasu jaruman mutane da suka gwada wata jarumtaka a rayuwarsu ko suka shiga wani ibtila’i ALLAH ya ku6utar dasu. Idan zan iya tunawa wasu daga cikin mutanen da akayi hira da su a cikin wannan shiri sun hada da Na Jalli Baban shirwa da Garba na Garba ga ruwa ga daji da Galadiman baka da Jangwalota baban karya da Ummarun Nakala Jan mutum mijin Mejidda da sauransu. Gaskiya na ji dadin hirar da Malam Baban Ladi ya yi da wadannan mutane saboda irin jarumtakar da suka nuna a matsayinsu na mafarauta da maharba da masunta. Hakika akwai abubuwa na mamaki da darasi a tattare da su.

MAITATSINE

Kamar sati 3 zuwa 4 da suka gabata shirin maza gumbar dutse ya tsunduma cikin labarin Metatsine. Ni dai ban san Metatsineba saboda a lokacin da akayi yakin Metatsine ina karamin yaro sosai ban san komai ba sai dai kawai na dan bibiyi tarihinsa amma a sanadiyyar wannan shiri yanzu nasan waye Metatsine saboda anayin hirar sane da wadanda suke ganau ba jiyauba wadanda abinda ya rutsa da su Metatsine ya kashe musu iyaye da mazaje da mataye da ‘ya’ya da ‘yan uwa. Daga cikinsu akwai wadanda ya kamasu ya ajiye su a gidansa suke ganin irin rashin imanin da yake aikatawa. Wani abu da tayarmin da hankali shine irin yadda yake yanka mutane ya sha jininsu kuma ya cire wasu sassa na jikinsu. Ya kashe yara da manya maza da mata wadanda ALLAH kadai yasan adadinsu. Mace me ciki yakan farke cikinta ya dauko Dan cikin ya yankashi ya yankata.

Tabbas Metatsine tsinannene, Dan iskane kafiri kuma Fir’aunane da akayi a Kano a unguwar Koki da ke cikin birnin Kano wanda ya tayarwa da mutanen Kano hankali kuma wai  yake wa’azi yana da’awar cewa shi Annabine. Daga karshe dai ALLAH ya kawo karshensa sojoji suka kashe shi a shekarar 1980 lokacin marigayi Alh Abubakar Rimi yana Gwamna a Kano kuma Alh Shehu Shagari yana shugaban kasa. Bincike ya tabbatar shi mutumin garin Marwa ne da ke Kasar Kamaru.

Ga duk mai son ya Ji wannan labari sai ya saurari Rahama rediyo f.m. (97.3) tare da Barden Madaki Alh Baban Ladi a duk ranar Laraba karfe 10 na dare zuwa 11.

ALLAH ka shiga tsakanin nagari da mugu.