
Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya, NPA, ta tabbatar da cewar wasu manyamanyan jiragen ruwa makare da manfetur sun iso gabar ruwan Najeriya. Hukumar kula da tashohsin ta bayyana hakan ne a Legas, a bayanin da take wallafawa kowace rana.
Hukumar ta kara da cewar, bayan shirgegen jirgin da ya iso gabar ruwan Najeriya da man fetur, akwai kuma wasu manya manyan jiragen dake dauke da takin zamani da sumea suke gab da isowa.
Sannan kuma, hukumar tace ana sa ran isowar wasu manyan jiragen ruwa guda 36 dauke da kayan abinci da sinadarai da sauran kayayyaki domin amfanin ‘yan Najeriya. Ana sa ran jiragen zasu iso tashar ruwa ta Apapa da kuma tsibirin nan na Tin-Can a tsakanin 10 zuwa 29 ga watan Janairun nan da muke ciki.
“Manya manyan jiragen ruwan da ake sa ran isowarsu akwai masu dauke da Alkama da manyan kwantenoni dauke da sukari da gishiri da daskararren kifi da gaz da sauran kayan tijara na ‘yan kasuwa” A cewar Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya.