
A rana mai kamar ta yau, Shekaru 51 da suka gabata, Nigeria ta tsinci kanta a wani irin mummunan yanayi, wannan halin da yayi sanadiyar da har yau kasar ke fama da shi na bambanci addini da kuma kabila. A wannan juyin mulki da akai ne ya haddasa kusan galibin matsalolin da suka dabaibaye wannan kasa, suka zamat mata wani irin mugun gyambo me wuyar magani. Domin kuwa, wannan juyin mulkin yayi sanadiyar Shahadar Firaminsta na farko kuma na karshe a tarihin wannan kasa wato Sir Abubakar Tafawa Balewa a Shalkwatar Gwamnatin tarayya dake Legas da kuma Firimiyan Jihar Arewa Sir Ahamadu Bello dake Kaduna tare da sauran jiga jigan mutane da manyan sojoji a kasarnan.
Yana daga cikin irin baiwar da Allah ya huwacewa Sir Abubakat Tafawa Balewa na iya magana da salo da sarrafa harshe a duk lokacin da yake gabatar da jawabi. Masana tarihi na lokacin sun cirawa Tafawa Balewa tuta, sannan zalakarsa ta janyowa wannan kasa mutunci da kima da kwarjini a idon duniya. Zamu shaida haka, idan muka duba yadda Sir Abubakar Tafawa Balewa ya samu tarba ta girmamawa a ziyararsa ta farko a kasar Amurka.
A daya bangaren kuma, Arewar Sardaunan Sokoto, wadda a yanzu ta koma jiha goma sha tara har da Abuja, tana cikin mawuyacin hali har yanzu Shekaru 51 bayan rasuwarsa. Da yawan Gwamnonin Arewa 19 da suka gabata da masu ci a yanzu, suna ta ikirarin kokarin kwatanta halaye irin na Sardauna amma babu wanda ya kama kafar Sir Ahamadu Bello Sardaunan Sokoto, abubuwa da dama da ya bari har yau ba a iya cigaba da su ba.
Na daga cikin muhimman abubuwan da Sardauna ya bari wa shugabannin baya, shi ne samar da ingantaccen Ilimi, ayyukan raya kasa, katafariyar Jami’ar ABU dake zaman irinta ta farko a kudu da hamada Sahara da kuma makekiyar kwalejin horar da kwararru dake Kaduna, wato Kaduna Politakanik.
Wannan juyin mulki na 15 ga Janairun 1966, ya mayar da hannun agogo bayan baya ga cigaban wannan yanki da wannan kasa, al’amura duk sun sauya komai ya tabarbare a Arewa musamman ilimi wanda rashin samun ingantaccensa yayi sanadiyar rura wutar gaba a tsakanin mutanan Arewa da hakan yakai ga samar da jihohi 19 na yanzu, wanda a baya Arewa guda daya ce. Allah ya jikan Sir Abubakar Tafawa Balewa da Sir Ahamadu Bello da Zakariya Mai Malari, Allah ka kyauta kwanciya a garesu, Allah kasa mutuwa hutu ce a gare su.
Haka nan, mutane irin su Samuel Ladoja Akintola da suka bayar da gudunmawa mai yawa domin dorewa da kuma cigaban wannan kasa, wanda suma suka rasa rayukansu a sanadiyar wannan juyin mulki, suma muna tunasu tare da tsinkayen irin harsashin da suka aza na samun Ingantacciyar Nijeriya.
Gimba Kakanda ya rubutu na fassara.
Yasir Ramadan Gwale
15-01-2017