
Hukumar yaki da cin hanci da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC, ta bayar da belin tsohon Sakataren Gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal.
Wata majiya a hukumar, ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, cewar, an bayar da shi beli ne a ranar Juma’a da yamma.
Majiyar dai bata yi karin bayani akan wannan belin da aka bayar ba.
Hukumar dai na tsare ne da tsohon Sakataren Gwamnatin tarayya, bayan da ya amsa gayyatar da hukumar tayi masa a ranar laraba.
Da kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ya tuntuni kakakin hukumar kan wannan batun bada belin, yace shi ma ba shi da masaniya.
Ana dai zargin Babachir da yin sama da fadi da kusan Naira miliyan 200 kudin yankan ciyawa da aka ware za’a yi a sansanin ‘yan gudun hijira, wadda ta kai har Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da shi.