
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai, yabara kan batun doguwar wasikar da tsohon Shugaban kasa Olushegun Obasanjo ya rubutawa Shugabankasa Muhammadu Buhari a makon da ya shige kan halin da kasarnantake ciki.
A ranar 23, ga watan Janairun nan, Mista Obasanjo ya fitar da wata wasika mai shafuka goma sha uku,inda a ciki yayi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da kada ya sake neman tsayawa zabe a shekarar 2019.
A yayin wannan sanarwar da Mista Obasajon ya bayar, ya bayyana gamsuwar da rashin ingancin Shugaba Buhari ya sake neman Shugabancin Najeriya a karo na biyu, inda ya bukaci Shugaba Buhari da ya hakura ya zama sahun tsaffin Shugabannin Najeriya kawai.
Sai dai wannan wasika ta Obasanjo ta tayar da kura a al’amuran siyasar kasarnan, inda ba tare da wani dogon lokaci ba Gwamnati ta mayar da martani amma cikin kamalai na dattako, inda ta bayyana irin nasarorin da Shugaba Buhari ya cimma a mulkinsa.
Amma a wani bayani da ya ruuta a shafinsa na Facebook a ranar lahadi, Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai, wanda ya taba rike mukamin darakta janar na hukumar sayar da kadarorin Gwamnati zamanin Mulkin Obasanjo, sannan kuma ya zama Ministan Abuja a karkashin Obasanjo, ya tofa albarkacin bakinsa.
“Sam ban karanta wannan wasika a Obasanjo ba, sabida ayi tsawo da yawa, kuma ina cikin rashin yalwar lokaci, ba zan iya karanta ta ba” El-Rufai ya bayyana haka a shafinsa na facebook a ranar lahadi.
“Ba ni da wata shakka kan cewar, zamu lashe zaben 2019 na Shugaban kasa. Sannan kuma zamu iya samun nasara a jihohinmuna APC”
“Mutanan Najeriya kashi biyu ne, akwai bangaren masu arziki, da kuma yaku bayi, wadannan yakubayin su ne zasu kuma zabenmu a 2019, amma fa sai Allah yaso”.