
Bayan wata zazzafar muhawara a zauren majalisar dattawa a ranar laraba, majalisar tace ba zata tattauna batun rikici tsakanin Kwankwaso da Ganduje ba, domin a cewar majalisar rikicin batu ne na cikin gida tsakanin Kwankwaso da Ganduje.
Sanatocin sunce duk wani abu da ya faru tsakanin Kwankwaso da Ganduje batu ne na cikin gida, sannan majalisar ta bukaci Sufeto janar na ‘yan sandan Najeriya da ya baiwa Sanata Kwankwaso cikakken tsaro a duk ranar da ya sanya zai shiga jihar Kano.
Da yake bayyana jawabi kan wannan batu, Shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki, yace ya saurari dukkan bangarorin da suke adawa da junatsakanin Kwankwaso da Ganduje, kuma yace al’amarin batu ne na cikin gida.
Saraki yace, a dukkan jihohin fadin tarayyar Najeriya, akwai sabani tsakanin tsohon Gwamna da sabon Gwamna, yace wannan sabani na Kwankwaso da Ganduje ba wani sabon abu bane, a sabida haka ba wani abu bane da majalisar dattawa zata mayar da hankali akansa domin tattaunawa ba.
Haka nan kuma, Mista Saraki, ya bukaci kwamaitin majalisar dattawa dake lura da sha’anin ‘yan sanda da ya gayyaci Sufeto janar na ‘yan sanda na kasa domin yayi musu bayanin yadda akai ya kasa baiwa Sanata Kwankwaso cikakkun jami’an tsaro a taron da ya shirya yi 30 ga watan da ya gabata.
Tun farko dai, Sanata Isah Hamma Misau daga jihar Bauchi ne, ya kawo batun gaban zauren majalisar dattawa inda yace akwai munanan hotuna dauke da muggan makamai, da aka dinga yadawa a shafukan sada zumunta na intanet, wanda aka ce an dauke su ne a Kano.
Sanata Misau yace, idan har za’a iya hana dan majalisar dattawa zuwa mazabarsa domin ganawa da al’ummar da yake wakilta, to lallai akwai matsala a kasarnan.
Yace,idan hotunan da muke gani suna yawo a shafukan sada zumunta na intanet game da kano gaskiya ne, to lallai rayuwar al’umma tana cikin hadari kwarai da gaske.
Yace a matsayina na Sanatan da ya fito daga Bauchi, wadda muka yi iyaka da jihar Kano, yace wannan shi ne dalilin da ya ja hankalinsa cewar, lallai abinda yaci doma baya barin Awe.
Daga nan Sanata Misau ya bukaci Sanatoci da su yi Allah wadai da abinda ya faru a Kano na kokarin dawo da siyasar daba da yawo da makamai.
Bayan da Sanata Misau ya gama jawabinsa, Sanata Kabiru Gaya daga Kano, yace ya caccaki Misau, inda yace duk irin abubuwan da suka gudanar a jihar babu inda aka tayar da rikici koo hatsaniya.
Yace duk wani sabani tsakanin Kwankwaso da Ganduje batu ne na cikin gida kuma za’a warware shi cikin sauki.