Home Labarai Miyagun ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane 38 sun shiga hannu a Kaduna

Miyagun ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane 38 sun shiga hannu a Kaduna

0
Miyagun ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane 38 sun shiga hannu a Kaduna

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kaduna, ta ci nasarar cafke ‘yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane su 38 wadan da suka addabi hanyoyi a Kaduna, an kame ‘yan fashin daga ranar 20 ga watan Oktoban 2017 zuwa 25 ga watan Janairun 2018.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna Mista Austin Iwar ne ya bayyana hakan a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a ranar Laraba.

Yace a cikin mutum 38 din da aka kama, 21 an kama su ne da kokarin yin garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa da ayyukan ta’addanci, 17 kuma an kama su ne da laifin sace sace na cikin unguwa da kuma ayyukan sara suka.

Yace, irin miyagun makaman da aka samu a wajensu, sun hada da Alburusai 41 da manyan motoci guda uku, sannan kuma rundunar ‘yan sanda ta ci nasarar tarwatsa wata maboyar ‘yan fashin a cikin daji.

Kwamishinan ‘yan sandan yace, abin farinciki a wannan kame da aka yi shi ne, an kama ‘yan fashin da suka addabi hanyar Kaduna zuwa Zariya zuwa Kano.

“Wasu daga cikin wadan da aka kama din, suna yin garkuwa da mutane a yankin Lere da Fambeguwa a yankin Kubau da Zaria”

Sannan kuma, yace, wadan da aka kama masu sace sace da sara suka an kama su ne a Rigasa da Tudun wada da Kawo da Unguwar Rimi duk a cikin birnin Kaduna.

Yace dukkan mutanan da aka ci nasarar kamawa suna nan a hannun ‘yan sanda suna bayar da bayanai, ‘yan sanda kuma na cigaba da gudanar da bincike, daga zarar an kammala bincike za’a gabatar da su gaban kotu don fuskantar hukunci.

“Muna son mu tabbatarwa da al’umma cewar, rundunar ‘yan sanda tana aiki babu dare babu rana wajen ganin ta kamo masu laifi a duk inda suke, da karya lagon dukkan wani aikin batagari” A cewarsa.

Sannan yayi kira ga al’umma da su baiwa rundunar ‘yan sanda hadin kai musamman wajen bayar da bayanan da zasu kai ga samun nasarar cin lagon miyagunmutane a ko ina suke.