Home Kanun Labarai Addinin Musulnci ba shi da alaka da bara da tumasanci da batun tashin hankali – JNI

Addinin Musulnci ba shi da alaka da bara da tumasanci da batun tashin hankali – JNI

0
Addinin Musulnci ba shi da alaka da bara da tumasanci da batun tashin hankali – JNI
Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sultan Sa'ad Abubakar III

Kungiyar Jama’atu Nasril Islam,JNI, a ranar alhamis ta bayyana cewar bara da tumasanci da roko ba su da wata alaka da addinin Musulunci, tace wannan ma sam bai dace ba a Musulunce a samu yara suna yi.

Ustaz Khalid Abubakar, Babban sakataren JNI na kasa, shi ne ya bayyana hakan a Kaduna a wani taron kasa da manyan limamai da ya gudana mai take “Kawo karshen cin zarafin kananan yara a Najeriya”

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewar, wannan shiri da JNI ta gudanar an shirya shine karkashin hadin giwa da USAID da kuma UNICEF.

Ustaz Abubakar yace, arbiyyar yara abu ne da ya shafi al’umma baki daya ba wasu mutane su kadai ko iyaye kawai ba.

“A muslunci, hakkin iyaye ne su tabbatar yaransu sun samu kulawa a karon farko, ankula da cinsu da shansu da tufatarwarsu har zuwa lokacin da zasu kai munzalin balaga, musamman a shekarun na farko tilas a kula da su”

“Kowanne yaro a Musulunci yana da ‘yancin samun Ilimi da ci da sha da kuma samun kariya daga kowacce irin cutarwa”

A cewarsa, yara suma wani bangare ne na iyali da kuma al’umma.

“Domin baiwa yara kulawa ta musamman don su zama manyan gobe, dole ne a janyo su a jiki tare da nuna musu muhimmancinsu a mu’amalancesu yadda ya dace”

A cewar JNI, hakkin kowanne yaro ne ya samu kariya daga aukawa kowanne irin nau’i na rikici wanda ka iya jefa rayuwarsa cikin hadari.

“”Musulunci ya bayar da ‘yanci ga kowa, gwargwadon yadda Musulunci ya tsara” A cewar Ustaz Abubakar

Haka kuma, ya lisafta wasu bangarori na tashin hankali wadan da addinin Musulunci ya katange kananan yara daga aukawa, misalin yunwa da azabtarwa da dukkan wani nau’i na cutarwa.

Sannan kuma, Sakataren JNI din ya kalubalanci iyaye da suke barin hakkin kulawar yaransu akan ‘yan aiki da masu yi musu aikatau.

Bayan haka kuma, Losunbpp Odebode babbanKodineta na VAC da UNICCEF ya bayyana cewar babbandalilin shirya wannan taro shi  ne don karawa Malaman addini kaimi da kuma nuna musu muhimmanci da martaba ta baiwa yara kulawa ta musamman, tare da kaucewa jefa su cikin rikici da sauransu.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewar, an shirya wannan taron ne domin Malaman addinnin Musulunci dake Arewacin Najeriya.

NAN