
Babban sakataren jam’iyyar ANC mai mulkin Afurka ta kudu Ace Magashule tare da mataimakinsa Jessie Duarte, sun gabatarwa da Shugaban kasar Afurka ta kudu Jcob Zuma yau a ofishinsa, takardar kin amincewa da shi a matsayin Shugaban kasar Afurka ta kudu a karkashin jam’iyyar.
Bayanai sun tabbatar da cewar, mutanan sun shafe kimanin mintoci 90 tare da Shugaba Zuma suna tattaunawa.
A halin da ake ciki yanzu, Jacob Zuma na cikin tsaka mai wuya na cigaba da zamansa Shugaban kasar Afurka ta kudu, kasancewar a watan da ya gabata jam’iyyar ANC ta zabi Cyril Ramaphosa a matsayin sabon Shugabanta.