Home Labarai Ma’aikatan ‘Nigerian Air Ways’ sun koka kan kin biyansu hakkokinsu

Ma’aikatan ‘Nigerian Air Ways’ sun koka kan kin biyansu hakkokinsu

0
Ma’aikatan ‘Nigerian Air Ways’ sun koka kan kin biyansu hakkokinsu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ware zunzurutun kudi Naira biliyan 45 domin a biya ma’aikatan rusasshen kamfanin jiragen sama na Najeriya ‘Nigeria Air Ways’ hakkokinsu, amma an gaza biyansu har yanzu a cewar Shugaban kungiyar ma’aikatan Abubakar Yusuf.

Tun a watan Disambar Shekarar da ta gabata ne, Shugaba Muhammadu Buhari ya mince da a yi amfani da Naira biliyan 45 domin biyan tsaffin ma’aikatan kamfanin hakkokinsu. Amma har kawo wannan lokaci babu ko mutum guda da ya karbi hakkinsa.

A wata takardar koke da tsaffin ma’aikatan suka aikawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari wadda DAILY NIGERIAN ta samu kwafi, Abubakar Yusuf yace, wasu manyan mutane ne a sama suke neman karkatar da akalar kudaden zuwa ga bukatun kansu.

A cewar manajan kamfanin shiyyar jihar Kano, Abubakar Yusuf, wasu mutane ne marasa gaskiya suka kanainaye abin suka hana a biya ma’aikatan hakkokinsu cikin lokaci, dan haka ake ta jan kafa.