
Hassan Y. A Malik
Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, ya karyata wani batu da ke yawo a kafafen yada labarai da ke bayyana cewa wai ya yi allawadai da dimbin albashin da ‘yan majalisar tarayyar Nijeriya ke dauka a duk watan duniya, sanadin da, kamar yadda sanarwar bogin ta bayyana, wai hadamar ‘yan majalisar ta taimaka matuka wajen hana matasan kasar nan aikin yi.
Wannan sabuwar sanarwa ta fito ta bakin shugaban ma’aikatan fadar Sarki Muhammadu Sanusi II, wato Munir Sunusi, a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a Kano.
Munir Sunusi ya ce, Sarkin Kano bai fitar da wata sanarwa da wancan taken ba kuma bai umarci wani ya yi wannan magana da yawunsa ba.
“Waccan sanarwa ba komai bace illa zunzuruntun karya da kazafi da kage da wasu marasa son zaman lafiya suka shirya kuma suke yada shi don su shiga tsakanin mai martaba sarki da masu alfarma ‘yan majalisar tarayyar Nijeriya.”
“A wannan rana da sanarwar ta fita, mai martaba, bai karbi wani bako ba kuma bai yi magana da ‘yan jarida ba, haka kuma bai fita daga fad aba, a saboda haka babu yadda za a yi a ce ya yi wata magana da ta shafi kasar nan da wani da har maganar za ta yadu a kafafen yada labarai,” inji Munir Sunusi.
Sarkin Kano ya bayyana cewa: “Ina mai sanarwa da al’umma cewa, tsakanina da ‘yan majalisar tarayyar Nijeriya da ‘yan majalisar jihar Kano ba komai sai fahimtar juna da girmama juna.”
“Kuma ma ai, bani da wani hakki na in shatawa gwamnati abinda za ta biya wani albashi. Wannan ko shakka babu tsari da ra’ayin gwamnati ne ta hukunta albashin ma’aikacinta.”
Sarki Sanusi ya yi kira ga manema labarai da a maimakon su ci gaba da kirkiro labaran kanzon kurage wadanda ba za su amfanawa zaman lafiyar kasar nan komai ba, kamata ya yi su zama jakadun wanzar da zaman lafiya.