
Wani rikici da ake kyautata zaton yana da nasaba da addini ya barke tsakanin Musulmi da Kirista a Kasuwar Magani dake yankin karamar hukumar Kajuru dake jihar Kaduna.
Thusday, ta ruwaito faruwar wannan al’amari, inda tace rikicin ya barke da misalin karfe 10 na safe a ranar Litinin.
Rikicin dai ya faru ne sakamakon garkuwa da wata da aka yi kuma aka tursasa mata bin addini a yankin.
Majiyar ta kara da cewar, an bankawa gidaje da dama wuta, yayinda mutane da yawa suka ji munanan raunuka a sakamakon kararwar da aka yi.
Tuni dai aka tura jami’an tsaro domin kwantar da tarzomar da ta barke.