Home Labarai Ziyarar jaje ba zata dawo da ‘yan matan da aka sace ba – Osinbajo

Ziyarar jaje ba zata dawo da ‘yan matan da aka sace ba – Osinbajo

0
Ziyarar jaje ba zata dawo da ‘yan matan da aka sace ba –  Osinbajo
Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osibanjo
 

Hassan Y.A.Malik

Mataimakin Shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana dalilin da ya sanya Shugaba Muhammadu Buhari bai ziyarci jihohin Yobe, Binuwai, da Zamfara don jajanta musu sakamakon kashe-kashen da aka yi baya-bayan nan da kuma sace ‘yan mata 110 a Dapchi ba.

Osinbajo, ya bayyana cewa shi da kansa ya wakilci shugaban kasa a wasu jihohin don jajanta musu a lokacin ibtila’i, wanda kuma haka ya wadatar ba lalle sai shugaban kasa ya yi kafa da kafa ba, domin kuwa shi zuwan shugaban kasa ba zai dawo da ran da aka rasa ba ko kuma mutane da suka bata ba.

 Game da batun ‘yan matan Dapchi kuwa, Osinbajo ya ce, “Abinda ya fi muhimmanci shi ne samar da tsaro ga makarantu a fadin kasar nan ba wai gaisuwar jaje bayan wani abu na rashin dadi ya faru ba, domin dai babu adadin jajen da zai dawo da abinda aka rasa ko a Calabar, ko a Mambila, ko a Binuwai, ko a Adamawa ko a Zamfara.”

Osinbajo ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da ya yi da manema labarai a jihar Legas a yau Lahadi, inda ya bayyana wuraren da ya wakilci shugaban kasa don jajanta wa al’umma bisa ibtili’in da ya same su.

“Na je Zamfara, na je Adamawa a lokutan da ak yi kashe-kashe a jihohin. Kuma ko a watan Satumbar shekarar da ta gabata sai da na ziyarci jihar Binuwai don jajantawa al’ummar jihar bisa wani kisa da aka yi a wancan lokacin, kuma mun yi nazari da duba kan abinda ya faru.”

“A baya-bayan an samu tashe-tashen hankula a wurare da dama ciki kuwa har da sace ‘yan matan Dapchi. Mun aika musu da jajenmu, cike da sanin cewa jajen namu ba zai dawo musu da ‘ya’yansu ba.”

“Abinda muke yi, wanda shi ne al’muhim, shi ne kokarin samar da tsaro a kasar nan. Wannan ya sanya muka tura soji bataliyoyi biyu na soja jihar Kaduna. A jihohin Binuwai da Taraba, mun tura bataliya ta 93 da bataliya ta 72 wadanda rundunoni ne na musamman

“Mun sanya idanu sosai, akan yadda abubuwa ke gudanawa a jihar Taraba don ganin cewa abubuwa ba su kazanta ba.

“Ni a gani na wannan shi ne ya fi muhimmanci, samawa ‘yan kasa tsaron rai, lafiya da dukiyoyinsu, amma ba wai batun waye ya je jajen ibtili’i, waye kuma bai je ba.”