
Ana cigaba da bayyana ra’ayoyi kan auren ‘yar Gwamnan KanoAbdullahi Umar Ganduje da dan gidan Gwamnan Oyo Abiola Ajimobi, yayin da tsohon Gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya shiga cikin masu magana kan wannan biki.
On Saturday,
A ranar Asabar, Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Shugaban majalisar dattawa ta kasa, Bukola Saraki da gwamnoni da Jagoran jam’iyyar APC na kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da manyan attajirai irinsu Aliko Dangote suka halarci daurin auren wanda aka yi a fadar mai Martaba Sarkin Kano,Muhammadu Sunusi na biyu.
A wani biki da aka yi na kasaita, Gwamna Ganduje ya bayar da auren ‘yarsa Fatima ga Idris Ajimobi, dan Gwamnan jihar Oyo, Mista Abiola Ajimobi.
A lokacin da yake shaidawa magoya bayansa a Kaduna, a ranar Asabar, Sanata Kwankwaso ya caccaki wannan aure, inda yace yarinyar fa Bazawara ce ba wani abu ba.
“Mutane kalilan ne suke farinciki da wannan aure, domin yarinyar dai Bazawara ce ba wata tsiya ba”
“”Mun ji cewar, dukkan hanyoyin shigowa cikin birnin Kano, sun kasance cike da jami’an tsaro sabida kawai auren wata ‘yar bazawara guda daya”
“Wannan kuma ba komai yake nunawa ba, sai irin yadda Kwankwasiyya take da matukar tasiri a jihar Kano”
Ya kuma bayyana cewar duk manyan bakin da suka halarci wannan daurin aure, duk ba su da aikin yi shi yasa suka je.
“Mun ji cewar mutane da yawa, sun bar uraren ayyukansu sabida ba abinda suke yi shi yasa suka zo daurin auren”
“Haka kuma, mun ji cewar, mutane sun batawa kansu lokaci domin halartar auren Bazawara”