
Hassan Y.A. Malik
Alkalin kotun majistare da ke zamanta a Ota, jihar Ogun ne ya yankenwa Femi wannan hukunci bayan da kotu ta same shi da laifuka biyu da suka hada da kutsawa cikin gini ba tare da ka’ida ba da kuma aika sata.
Alkalin, Mai shari’a B.B. Adebowale ya yankewa Femi hukuncin daurin shekaru biyu ba tare da zabin biyan tara ba, inda ya bada dalilinsa na yanke wannan hukunci da cewa, laifin na Femi ya saba da sashen doka na 415 da na 516 na kundin laifukan jihar Ogun.
Mai gabatar da kara, Abdulkareem Mustapha ya bayyanawa kotu cewa wanda ake kara ya aikata laifin ne a ranar 19 ga watan Fabrairu da misalin karfe 3:30 na dare, a cocin Celestial Church da ke Joju, a Ota.
Mustapha ya ci gaba da cewa, Femi ya kutsa kai cikin cocin kuma ya saci wayoyin hannu da dama mallakar mabiya cocin, da aka yi kiyasi darajar ta kai Naira dubu 150.