Home Labarai Mutanan Arewa sun kare da kuturun bawa a wannan Gwamnati – Buba Galadima

Mutanan Arewa sun kare da kuturun bawa a wannan Gwamnati – Buba Galadima

0
Mutanan Arewa sun kare da kuturun bawa a wannan Gwamnati – Buba Galadima

Tsohon na hannun daman Shugaba Buhari, kuma tsohon Shugaban yakin neman zabensa a baya, Injiniya Buba Galadima ya soki lamirin wannan Gwamnati kan yadda ta mayar da hankali kan kudancin Najeriya wajen cin ribar ayyukan raya kasa, da kuma romon demokaradiyya.

Buba Galadima ya caccaki wannan Gwamnati kan yadda ta fifita yankin kudu wajen gina manya manyan hanoyi ta kyale hanyar Abuja zuwa Kano, inda hanyar ta zama tarkon mutuwa da sace mutane.

A cewarsa, wannan Gwamnati ta amince da gina hanya mai tsawon kilomita 120 daga Legas zuwa Kala akan kudi Naira biliyan 300, yayin da ta yi shakulatun bangaro da hanyar Abuja zuwa kano.

Buba Galadima yana magana ne a wani faifan bidiyo da ya zagaya sosai a shafukan sada zumunta na intanet. Inda yace, wannan Gwamnati ta sanya hanyar ABuja zuwa Kano a cikin kasafin kudi, amma har yanzu bata bayar da umarnin fara aikin ba, yayin da take ta kokarin ganin ta bayar a kudancin kasarnan.

Ya cigaba da cewa,asali hanyar Legas zuwa Kalaba an bayar da ita ne akana Naira biliyan 100 amma daga bisani aka ninka kudin yakai har Biliyan 300, yayi da aka nunawa Arewa ko in kula.

Bayan haka kuma, Buba yace, wannan Gwamnati ta sake amincewa da gina hanyar Legas zuwa Ibada, wanda ake sake aikin ginin hanyar gaba daya.

Mista Galadima ya nuna damuwarsa kan yadda Arewa take neman karewa da kuturun bawa kan ayyukan raya kasa. Duk da cewar Shugaban kasa dan Arewa ne, amma bai nuna damuwa kan ayyukan raya kasa a Arewa ba.

A cewarsa, muna son ganin manyan ayyukan tituna a Arewa kamar yadda muke gani ana yi a kudu. Ya cigaba da cewar, ya kamata hanyar Abuja zuwa Kano a sake yin sabuwa ne fil kamar yadda ake yiwa hanyar Legas zuwa Ibadan, ba wai kwaskwarima za a yiwa hanyar ba.

Buba yace, muna fadin haka ne domin soyayyarmu da wannan Gwamnati, da kuma fatanmu na ganin ta sauka lami lafiya, yace babu yadda za’a yi muyi shiru ana yi mana irin wannan yankan baya haka, ana cewa Shugaban kasa namu ne dan Arewa, amma wasu ne can suke amfanarsa.

Ni bana cikin masu yin munafurci naja baki na tsuke dan dan Arewa ne yake Shugabanci a kasarnan, ko waye matukar yayi ba daidai ba zan fito na gaya masa gaskiya. A cewar injiniya Buba Galamida.