Home Labarai UTME 2018: Wasu tagwaye sun fada komar jami’an tsaro sakamakon magudin jarabawa

UTME 2018: Wasu tagwaye sun fada komar jami’an tsaro sakamakon magudin jarabawa

0
UTME 2018: Wasu tagwaye sun fada komar jami’an tsaro sakamakon magudin jarabawa

Wasu ‘yan tagwaye da suka yi matukar kama da juna sun shiga komar jami’an tsaro sakamakon magudin jarabawa da suka yi a yayin da ake rubuta jarabawar shiga jami’ah ta UTME. Matasan an kama su ne a jami’ar Maiduguri yayin daya ya zaunawa daya jarabawa.

Jami’in gudanar da jarabawar, Babagana Gutti, shi ne ya bayyana cewar jami’an tsaron suna tsare da tagwayen sakamakon magudin da suka yi a jarabawar da aka rubuta a ranar Asabar.

Mista Babagana Gutti, ya bayyana cewar, tagwayen sun yi matukar kama da juna sosai da gaske, yace daya daga cikinsu ne ya zaunawa daya jarabawa.

Jami’an da suke kula da tsarawa da shiryar jarabawar ta UTME, sun bayyana sunayen tagwayen da Hussaina Hassan Abdulhameed. An kama su ne, bayan da daya yaje aka tantance shi ta hanyar na’ura mai kwakwalwa, inda bada bisani bayan tantance shi yaja da baya dan uwansa ya shiga ya zauna masa a dakin jarabawar.

“Bamu fahimci cewar daliban suna shirya magudin jarabawa ba, sai lokacin da jami’in da yake kula da daliban, ya hangi daya a cikin dakin jarabawa dayaa kuma a waje”

“Na jima mamaki lokacin da na hangi dayan a waje, na kira shi nayi masa wasu ‘yan tambayoyi,amma ban gamsu da amsoshin da ya bani ba, daga nan ne na hada su tare domin tantancewa”

“Bincikenmu ya tabbatar mana da cewar, wanda yake cikin dakin jarabawar, yana rubutawa abokin tagwaitakarsa jarabawar ne” A cewar Mista Gutti.

Daga nan ne aka hannanta wadannan tagwaye zuwa ga hannun jami’an tsaro domin hukunta su.

Ya kuma bayyana cewar anyi jarabawar lami lafiya babu wata damuwa a ciki a jjihar Borno baki daya.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito cewwar, akalla dalibai 1,700 ne suka rubuta jarabawar a santocin jarabawar guda takwas da ake da su a jihar Borno.

NAN