Home Labarai Etsu Nupe ya yi Allah wadarai da Gwamnatin APC a jihar Neja

Etsu Nupe ya yi Allah wadarai da Gwamnatin APC a jihar Neja

0
Etsu Nupe ya yi Allah wadarai da Gwamnatin APC a jihar Neja

Daga Hassan Y.A. Malik

Shugaban majalisar sarakuna ta jihar Neja, Etsu Nupe (Sarkin Nupe), Alhaji Yahaya Abubakar, ya zargi gwamnan jihar ta Neja, Abubakar Sani Bello da rashin sanin makamar aiki.

Etsu Nupe ya zargi gwamantin ta APC da mayar da hankali wajen dadadawa iayalansu da makusantansu kadai a yayin da sauran al’ummar jihar ke fama da kuncin rayuwa.

Basaraken ya bayyana hakan ne a fadarsa da ake kira da fadar Wadata a lokacin da wata kungiyar gamayyar kabilun jihar mai rajin kyautata al’adu da siyasar jihar mai suna Gbapeko ta kai masa ziyarar ban girma a fadar tasa.

Etsu Nupe ya koka kan yadda abubuwa suke dada tabarbarewa a karkashin jagorancin wannan gwamnati, ta yadda al’umma ke ta dada shiga halin ni ‘ya su.

Etsu Nupen da ya samu wakilcin Wamban Nupe, Mahmud Abubakar, ya bayyana cewa dukkan titunan da suka hada garuruwa da kuma wadanda suka hada jihar Neja da sauran jihohi sun lalace matuka kuma gwamnati babu abinda ta ke yi a kai.

Shi ma sanata mai wakiltar jihar Neja ta gabas, Sanata david Umaru, a jiya Laraba, ya kalubalanci salon mulkin Gwamna Abubakar Sani Bello.

Sanata David ya shaidawa jaridar Guardian a wata hira da suka yi cewa: “Gwamnatin APC a jihar Neja ba ta tsinanawa al’ummar jihar komai, a saboda haka ma kar gwamnatin ta fara tunanin yin tazarce.”

“Babu wani aiki a kasa da zai saka gwamnatin ta nemi ta sake dawowa a 2019. Ina matukar takaicin kasancewa daya daga cikin wadanda suka kawo gwamnatin nan karagar mulki sakamakon rashin muhimmatar da damarta da gwamnatin take yi.”