
Daga Yusuf Dingyadi, Sokoto
Na dade ina nazari dangane da irin yadda matsalar karancin ruwan fanfo a birnin Sakkwato ta azzara, mussaman ga yadda lamarin ya koma na rashin sanin hanyar bullo ma matsalar da neman ko da akwai wata hanyar rage wannan lamarin ko magance ta baki daya; tun ma ba daga ita kanta Hukumar Kula da Samar da ruwan sha ta jahar Sokoto har ya zuwa ga Ma’aikatar Ruwa da albarkatunsu ba.
Abin ban takaici ganin cewar lamarin ya fara daga matsalar da ake iya yiwa jama’a bayani har ya azzara zuwa fiye da kwanaki sittin (60) ana ci gaba da fuskantar wahala da rashin sanin makoma, kamin sa’ilin gwamnati ta fara nuna damuwa ko daukar mataki akan wannan matsalar.
Shi kanshi Kwamishinan dake kula da ma’aikatar ruwa Alhaji Muhammadu Arzika Tureta ya ja bakinsa ya tsuke, har lokacin da masu sharhi a shafin zumunta na Facebook da kafofin yada labarai na rediyo suka fara tattauna matsalar da yin korafi akan sakaci da wannan lamarin kamin ya fito yayi bayani akan dalilan karancin ruwan ga al’ummmar Sakkwatawa.
Karancin ruwan sha a birnin Sakkwato, mussaman irin wannan lokacin ba wani sabon abu bane ga masana, duk da yake an dade ana samun irin haka daga matsalolin lallacewar injunan tace da tura ruwan sha zuwa ga manyan bututun dake kai ruwan a unguwanni da mahadar rarraba su, akan danganta matsalar daga karancin wutar lantarki ko karancin magungunan da ake amfani dasu wurin tace ruwa ko yawaitar matsalolin turo ruwa daga babban dam na Goronyo ko gulaben Rima.
MATSALAR DIMMAMAR YANAYI DA KUSKUREN NIMET
Ga bayanin da gwamnatin jahar Sokoto tayi, wannan matsalar karancin ruwan sha ba daga laifinta bane, don kuwa daman ana dogara ga samun ruwan da za a rarraba ma al’umma daga babban dam din Goronyo dake da yawan ruwa da tun farko ake turawa zuwa Kogin Rima da sauran kananan gulabe; mussaman wadanda ake kwasar ruwan zuwa babban bututun da Hukumar ruwan sha ta hada don kaiwa ga mahadar da ake tace su zuwa ga jama’a.
Wannan dam din yana da karfin aje ruwa har kubik mita miliyan dari tara da arba’in (940,000,000 cubic meter) wadanda cikinsu ake baiwa manoman rani da kuma wasu a jahar Kebbi don gudanar da ayyukan noman rani.
Da yake a baya anyi wasa da lamarin bayan Hukumar Kula da Yanayi ta kasa, NIMET tayi gargadi akan yiyuwar samun ruwan sama masu yawa da zasu yi barazana da janyo matsala ga dam din, lamarin da ya janyo bayar da umurni rage yawan ruwan da toshe hanyoyin shigowarsu zuwa ga dam tare da bude hanyoyin fitarsu anan take.
A cikin haka ne aka fuskanci matsalar dimamar yanayi wanda ya kawo karancin ruwan sama a wasu sassa masu yawa, har ma da ruwan dake zuwa ga dam din, don ko ya dogara ga samun ruwan nasa ta wasu mahadar ruwan daga gulabe masu yawa.
Hakan ya sanya ruwan na dam din suka yi karanci ga samarwa manoma rani da wasu yankunnan da ake tura su da issasun ruwa, abin da ya janyo karanci da yawan bukata ga lamuran noman rani da baiwa jama’a ruwan da zasu sha.
Sakamakon bayanin hukumar NIMET inji hujjojin gwamnati, hakan ya janyo an bar Dam din na Goronyo da karancin ruwa wadanda basu zarce akalla kubik mita guda miliyan dari ba (100, 000, 000 cubic meters). Wannan lamarin ya janyo karancin ruwa ga wasu ayyuka da akeyi ta amfani da dam din tare da rage karfin ruwan da zasu je ga wasu sassa da suka dogara da ruwan, mussaman gulaben da suke tsotsa ruwa da kaisu mahadar kogin Rima don baiwa Sakkwato ruwan sha.
Sai dai duk da hasarar kusan kubic miliyan dari takwas (840,000,000 cubic meters) bai janyo hankalin gwamnatin jahar Sokoto ta hannun hukumar samarda ruwan sha da wuri-wuri ba, don daukar mataki na gaggawa watani har kusan hudu da fara fusknatar karancin ruwan dake zuwa a ainihin manyan tankunan aje ruwa na hukumar dake gidan ruwa ba.
Wannan shine babban sakaci da rashin kulawa da hukumar ruwan sha da masu lura da ayyukan samar da ruwan suka yi; abin da ya janyo yanzu mafi rinjayen jama’a na cikin masifar karancin ruwan sha da na amfani a wurare dabam daban na birnin Sakkwato da kewaye.
Kusan a farkon lokaci na gyara da sake tsarin hanyoyin tace da rarraba ruwan sha ga al’ummar Sakkwato, an baiyana ana bukatar kusan galan miliyan biyu zuwa ukku kowace rana na ruwan sha ga birnin na Sakkwato da kewaye, abin day a janyo habaka na bukatar ruwa don amfanin yau da kullum.
Hukumar ruwan sha din da ake ganin tana fuskantar karancin kwarrarun masana da ma’aikata akan fanin ruwa da bincike ta koma tamkar wurin zaman hira da jiran tallafin gwamnati, don kuwa kudaden shiga na sayar da ruwan sha din bai iya gudanar mata da ayyukanta koda kuwa na mako biyu.
MAKUDAN KUDADE BABU AMFANI A FILI?
Wani bayani maras tabbas daga wata majiya ya baiyana a kusan kowane wata gwamnatin jahar Sokoto tana fitar da zunzurutun kudade har naira miliyan dari da saba’in da shida (N176,000,000) wajen gyara da tace ruwa tare da biyan kudaden wutar lantarki da na ayyukan mussaman ga hukumar samar da ruwan sha wadda bata wuce tara naira miliyan arba’in (N40,000,000) na kudaden ruwa a shekara ba.
Wadanan kudaden basu cikin na biyan magunguna da wasu ayyukan mussaman na shekara shekara, inji majiyar.
Hakika sakaci da rashin kulawa na hukumar tare da hadin guiwar ma’aikatar samar da ruwa na daga cikin dalilan da yanzu ya janyo al’umma suka fada cikin wannan wahalar ta karancin ruwan sha, fiye da irinsa a kusan tarihin samar da ruwan sha a jahar Sokoto.
RIJIYOYIN BURTSATSE
A watanin baya aka bayar da rahoton bayar da kwangilar gina rijiyoyin burtsatse irin na zamani har guda dari da hamsin (150) sai dai tun lokacin har yanzu babu labarin guda nawa aka gina ko a daya daga cikin yankunan da suka fi shan wahalar ruwan sha na birnin Sokoto.
Da ache an kammala wadanan rijiyoyin cikin lokaci zuwa yanzu da al’ummar Sakkwatawa basu koka akan matsalar karancin hanyoyin samun ruwa a gidajensu ko yadda zasu samu ruwan na sha ba.
Tsarin da gwamnatin take son bi a yanzu na sake gyara da bunkasa rijiyoyin tuka-tuka ko na hannu har guda saba’in da tara (79) zai rage raddadin ne na dan lokaci, ammam muhimmin abu shine ayi gyaran da zai dore a cikin lokaci muddin ana son kawo karshen karancin ruwa baki daya.
MAFITA
Haka ma akwai bukatar kulawa ga amfani da tankoki na mota a cikin birnin Sakkwato da kewaye don rarraba ruwa tamkar irin yadda gwamnatin jahar Zamfara tayi amfani dashi da aka samu mummunan matsalar ruwan sha a dam din wanke dake bayar da ruwa ga garin Gusau.
Sai kuma sake gyara da inganta manyan tankokin aje ruwa wadanda aka gina a lokacin gwamnatin Attahiru Bafarawa a tsohuwar kasuwa don aje da kuma tura ruwan da al’umma suke bukata.
Akwai bukatar a kusan kowane wata akwai akalla galan na ruwa har miliyan dari biyu da saba’in ga wadanan tankunan don taimakawa samar da issasun ruwa ga birnin na Sakkwato. Haka ma tankokin dake Ali Akilu na bukatar kulawa don inganta aje ruwan da zai amfani kusan manyan ungunwanin da yanzu haka suke cikin bukata.
Sai kuma fito da hanyar bunkasa aikin ruwa na Asari wanda tsohon gwamna aliyu Magatakarda Wamakko yayi, don kara yawan hanyoyin da jama’a zasu amfana ga ruwan sha.
KALUBALEN DAKE GABAN GWAMNA
Wani abin damuwa shine lokaci yayi da gwamnan jahar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal zai zage damtse wajen ganin ya fito da tsare tsare na gyara ga hukumar samar da ruwan sha da ita kanta ma’aikatar ruwan ta yadda za a baiwa masana daman shigowa su bayar da gudumuwarsu.
Gwamna Tambuwal ya sani yana da aiki mai yawa akan wannan lamarin, don kuwa duk matsalar da za a fuskanta a jahar Sokoto, tana da sauki bisa ga matsalar ruwan sha da lamarin tsaro. Da yake lamari tsaro bai da barazana a yanzu, ya dace ya mayar da hankali ga hanyoyin bunkasa samar da ruwan sha ga al’ummarsa.
KO ANA YIWA GWAMNA ZAGON KASA NE?
Masu yi masa zagon kasa da wadanda ake ganin suna murna ga faruwar wadanan wahalolin, ya dace ya dauki mataki na karshe akan lamarin. Ya sani fa muddin zai iya gyara to kuwa za a rage wahala, ko kuma ya ci gaba da fuskantar rashin amincewa daga al’ummar dake wahala daga wannan masifar.
Ya dace ta kasance muhimmin darasi da kalubale garesa da duk wadanda keda alhakin kulawa da samar da ruwan sha ga al’umma. Ta haka zai taimaka a kawo karshen wadanan wahalolin da suka janyo koma baya ga karatun dalibai da yiwa rayukan al’umma barazana da irin cuttutukan da ake gani na iya bulla idan aka ci gaba a haka.
Ruwa abokin rayuwa, yana da kyau gwamnati tayi hobbasa ga ganin lamarin ya zama sauki.
Yusuf Dingyadi, Dan jarida ne mai zaman kansa a birnin Sakkwato.