Home Labarai Kano: Sake fasalin fanshon tsaffin Gwamnoni bita da kulli ne ga Kwankwaso

Kano: Sake fasalin fanshon tsaffin Gwamnoni bita da kulli ne ga Kwankwaso

0
Kano: Sake fasalin fanshon tsaffin Gwamnoni bita da kulli ne ga Kwankwaso

Wani tsohon dan majalisar dokokin jihar Kano, wanda ya nemi a sakaya sunansa, yace wannan yunkuri na sake fasalin fanshon da ake baiwa tsaffin Gwamnoni da mataimakansu da majalisar dokokin jihar Kano ta bijiro da shi ba komai bane face bita da kulli ga Kwankwaso da sauran tsaffin Gwamnoni.

A ranar Litinin ne, majalisar dokokin jihar Kano ta fara wani yunkuri na sake fasalin fansho da garatuti da ake baiwa tsohon Gwamna da mataimakinsa, wannan batu ya biyo bayan wani kudiri da dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Warawa a majalisar dokokin jihar Kano, Labaran Madari ya gabatar.

Haka kuma, tsohon dan majalisar ya bayyana cewar, bayan an shafe lokaci ana ta kiran a sake fasalin wannan doka, ba a yi hakan ba, sai yanzu da aka ga alaka ta yi tsami tsakanin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Kwankwaso.

A cewarsa, wannan kuduri ba komai bane face kokarin munanawa Sanata Kwankwaso da ake son yi.

“Wannan yunkuri abu ne da aka shirya shi, domin cin zarafin tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso domin a tunaninsu zasu rage masa kima” A cewarsa.

Bayan haka kuma, wata kungiyar da ba ta Gwamnati ba a jihar Kano mai suna Muryar Matasa masu rajin kawo cigaba, ta yi maraba da wannan kuduri, a cewarsu wannan abu ne da aka jima ana jiransa.

Lokacin da DAILY NIGERIAAN ta sake duba wannan doka a sashi na 3 karamin kashi na 1 dokar ta tanadi biyan Gwamna da mataimakinsa fansho da ya kai kimar abinda Gwamna mai ci yake samu a shekara guda.

A yanzu haka, Gwamna yana samun Albashin da bai gaza Naira miliyan 2.22 ba duk wata, yayin da mataimakinsa yake samun 2.11 duk wata.

Daga cikin abubuwan da tsaffin Gwamnoni zasu amfana da shi a cewar wannan doka, akwai sabbin motoci guda biyu na zamani wanda za’a dinga canzawa Gwamna su duk bayan shekaru 4, tare da bashi mai tukashi, da cin gajiyar zuwa jinya shi da iyalansa a ko ina a fadin duniya.

Haka kuma, dokar ta tanadi cewar, tsaffin Gwamnoni zsu dinga tafiya hutun karshen shekara na kwanaki 30 a cikin najeriya ko a wajenta, sannan kuma da samar musu katafaren Ofis a duk inda suke so a fadin Najeriya.

Me zaku ce kan wannan batu?