
‘Yan kungiyar Boko Haram wadan da suka rako ‘yan matan makarantar Dapchi zuwa gida sun shafe tsahon mintuna 20 a cikin garin na Dapchi suna kiran mun dawo da ‘yan matan a muka sace.
Wani da ya shaida abin akan idonsa, yace da sanyin safiyar wannan rana ta Laraba ne ‘yan kungiyar ta Boko Haram suka shigo garin na Dapchi cikin shigar yaki, amma basu taba kowa ba.
“Lokacin da suka shigo babu wani alamun tsoro ko razana a tare da su,. Sune suka umarci ‘yan matan da su sauko daga cikin motocin da aka kawo su, sannan suka tara su a waje daya, suka dan yi musu wa’azi”
“Sun yi musu wa’azin su ji tsoron Allah, su daina neman ilimin boko su kama hanyar Allah shi kadai”
“Sun shaida musu cewar sun dawo da su ne, saboda su basu damar komawa zuwa ga Allah” Wani da abin ya faru a gabansa ya shaidawa DAILY NIGERIAN.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta tabbatar da sakin ‘yan mata 76 a cikin 110 daga cikin daliban da aka sace da sanyin safiyar wannan rana.
A wata sanarwa a Abuja a ranar Laraba, Ministan yada labarai da al’adu na tarayya Alhaji Lai Mohammed, ya ce dalibai 76 sun shaki iskar ‘yanci a wannan rana ta yau.
A cewarsa, 76 da aka saki a yau din, sune wadan da ake da sunayensu a rubuce, yace nanba da jimawa ba za’a saki sauran daliban da aka sace din.
Yace an saki ‘yan matan da misalin karfe 3 na Asubah, ta hanyar wasu muhimman mutane da suka taimakawa najeriya wajen ganin an saki ‘yan matan da aka sace din. An saki ‘yan matan ne ba tare da gindaya wasu sharudda ba.
“Gwamnati ta tabbatar da cewar amfani da karfin soja ba zai taba warware wadannan matsaloli na tsaro a Najeriya ba, shi yasa domin kada a illata wadannan ‘yan matan ba a yi tunanin amfani da karfin bindiga ba, shi yasa aka gwammace mika kai domin samun ‘yancin yaran”