Home Siyasa Sama da mutane dubu 100 sun sauya sheka daga APC da PDP zuwa SDP a Adamawa

Sama da mutane dubu 100 sun sauya sheka daga APC da PDP zuwa SDP a Adamawa

0
Sama da mutane dubu 100 sun sauya sheka daga APC da PDP zuwa SDP a Adamawa

Daga Hassan Y.A. Malik

Sama mutane dubu 100 ne suka sauya sheka a jihar Adamawa daga jam’iyyunsu na APC da PDP suka koma jam’iyyar SDP da tauraronta ke ci gaba da haskawa.

Shugaban jam’iyyar ta SDP, Cif Olu Falae ne ya bayyana hakan a yayin bikin karbar wadanda suka sauya shekar bisa jagorancin Cif Emmanuel Bello da aka gudanar a Lamido Sinima a jihar Adamawa.

“Na zo na karbi Cif Emmanuel Bello da dubunnan magoya bayansa da wasu da dama da suka bar APC da PDP zuwa jam’iyyarmu ta SDP a wannan jiha ta Adamawa.

“Jam’iyyar SDP ba sabuwar jam’iyya bace, ita ce jam’iyyar da MKO Abiola da Baba Gana Kingibe suka ci zabe a cikinta a shekarar 1993,” inji Falae

Da ya ke jawabi a wajen taron, Mista John Nuhu ya bayar da kididdigar adadin mutanen da suka bar APC da PDP zuwa SDP da kuma yankunan da suka fito.

“Daga Yola ta arewa akwai mutane 2,500, mutum 10,000 daga Gombi, 10,000 daga Song, mutum 5,000 daga Hong, mutum 3,000 daga Fofure, mutu 10,000 daga Demsa, wasu 10,000 daga Numan, wasu 10,000 daga Lamurde, 1,000 daga Guyuk, mutum 5,000 daga Shelleng, mutum 10,000 daga Jada, 10,000 daga Ganye.”

Har lau, akwai wasu mutane 20,000 daga Mayo, 10,000 daga Mubi ta arewa, 10,000 daga Mubi ta kudu, wasu mutum 10,000 daga Michika, 10,000 daga Madagali, 5,000 daga Maiha, mutum 5,000 daga Girei.

Wani jigo a jam’iyyar ta SDP, Farfesa Jerry Gana ya bayyana cewa wannan ita ce fitar jam’iyyar ta farko a wannan shekarar ta 2018.

Ya kara da cewa jam’iyyar SDP ta dauki aniyar kawo sauyi na gaskiya a Nijeriya.