
Sufeton ‘yan sanda na kasa, Ibrahiim K. Idris, ya janye batun da yayi a baya na janye dukkan ‘yan sandan da suke tare da manyan mutane da kamfanunuwa harzuwa nan da 20 ga watan Afrilu.
DAILY NIGERIAN ta ruwaito Sufeton a ranar 19 ga watan Maris yana mai bayar da umarnin janye dukan wasu ‘yan sanda da suke tare da wasu manyan mutane ko kuma kamfanunuwa a duk fadin Najeriya.
A wata sanarwa da ta fto daga mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta kasa, Jimoh Mshoodd ranar Alhamis a Abuja, Sanarwar tace jingine batun a yanzu da Sufeton yayi ya biyo bayan wata tattaunawa da yayi da kwamandan rundunar tsaro na ko ta kwana, da sashin da ke bincikar ayyukan ta’addanci, da jami’an masu bayar da kariya ta musamman.
Mista Mshood, ya bayyana cewar, wannan jinginewar zata baiwa rundunar damar yin nazari na musamman kan wannan batu da kuma tunanin daukar mataki na gaba kan wannan batu da yja hankali sosai.
Yace mataimakin Sifeto janar na ‘yan sanda mai lura da sashin ayyuka, ya sanar da dukkan kwamishinonin ‘yan sanda na jihohi da kwamandojin ‘yan sanda na shiyya shiyya da su jingine batun zuwa sabuwar ranarda aka sanya.
Sannan kuma ya bukaci ‘yan siyasa da manyan masu rike da mukamman Gwamnati da su cigaba da kula da ‘yan sandan da suke tare da su har zuwa lokacin da aka sanya na gaba.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ta ruwaito cewar Sifeto janar na rundunar ‘yan sandan na najeriya yana mai cewar zasu rubuta takarda zuwa ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari don sanar da shi da kuma neman Amincewarsa.
NAN