Home Labarai Kotu ta tisa keyar mutumin da ya yi wa ‘yar makwabcinsa fyade gidan yari

Kotu ta tisa keyar mutumin da ya yi wa ‘yar makwabcinsa fyade gidan yari

0
Kotu ta tisa keyar mutumin da ya yi wa ‘yar makwabcinsa fyade gidan yari

Daga Hassan Y.A. Malik

Kotu ta tisa keyar wani mutum da aka bayyana sunansa da Adamu Garba, dan kimanin shekaru 45 da haihuwa kuma dan asalin kauyen Gunduwawa da ke karamar hukumar Kankara, jihar Katsina zuwa gidan maza sakamakon zarginsa da laifin yi wa ‘yar makwabcinsa mai shekaru 13 fyade.

Rahoton ‘yan sanda ya bayyana cewa, Adamu Garba ya ja ra’ayin yarinyar zuwa cikin gidansa inda daga bisani ya yi lalata da ita ba da son ranta ba.

‘Yan sanda sun bayyana cewa laifin da ake zargin Adamu da sgi ya saba sashen doka na 283 na kundin pinal kod (penal code laws).

Mai shugar da kara a madadin hukumar ‘yan sanda, Insifeto Sani Ado ya bayyanawa kotu cewa har yanzu ‘yan sanda basu kammala bincike kan zargin ba, dalilin da ya sanya ya bukaci da kotu ta daga sauraron karar har sai sun kammala bincikensu.

 Mai shari’a Hajiya Fadila Dikko, bayyan sauraron rokon ‘yan sanda ta daga sauraron karar zuwa ranar 24 ga watan Afrilu, 2018, inda ta umarci da a tura Adamu Garba zuwa gidan yari har zuwa lokacin.