
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA ta shaida cewar ta karbi ‘yan Najeriya 149 wanda suka dawo Najeriya daga kasar Libiya bisa radin kansu.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta tabbatar da cewar, wadan da suka dawo din sun sauka a filin sauka da tashin jiragen saman Murtala Mohammed dake Legas, a wani jirgin shata mai suna Buraq mai Lamba 5A-DMG.
Jirgin ya sauka da misalin karfe 10:45 na yamma a wajen saukar kayayyaki na filin jirgin saman Mutala mohammed.
Mutanan da suka dawo sun hada da mata 37 da kuma Maza 107, mafiya yawancinsu sun dawo ne dalilin fama da rashin lafiya da suke yi.