
Daga Hassan Y.A Malik
Wata mace ‘yar Nijeriya da a ke zargi da juya akalar wasu gungun mata da aka yi safararsu daga Nijeriya zuwa kasar Spaniya don yin sanar’ar karuwanci ta shiga hannun jami’an tsaro a birnin Manchester ta kasar Ingila.
Ana zargin matar da zama daya daga cikin jagororin kungiyar asirin nan mai aika manyan laifukan nan ta ‘Eiye Confraternity’ da munanan ayyukansu ya shiga kasashen Nijeriya, Libya, Italiya da Spaniya.
Kafar yada labari ta Manchester Evening News ta rawaito cewa masu bincike sun gano mata 39 a kasar Spaniya da ke kwana a kogunan duwatsu da sauraren wuraren da babu cikakken tsaro ga lafiyarsu.
Hukumar Lura da manyan Laifuka ta Burtaniya NCA ta bayyana cewa dukkannin mata 39 da aka kama ‘yan Nijeriya ne da bincike ya nuna cewa an kaddamar da matar ne da tsafin voodoo-style don kar su saba dokokin da wadanda suka fitar da su.
An kuma fita da su daga Nijeriya zuwa Libya ta hanyar kwale-kwale. Daga Libya zuwa Italiya zuwa Spaniya.
Da dama daga cikin ‘yan matan ‘yan kasa da shekaru 18 da haihuwa ne kuma tsafin da aka yi akan su a lokacin kaddamar da su a kungiyar zai saka ba za su taba jin suna son barin inda aka kawo su ba don biyan bukatar maza ta hanyar jima’i, inda kudaden da aka tara dafa wannan cin zarafi na ‘yan matan za a dawo da su Nijeriya.
Kalli bidiyon yadda aka kama matar: