Home Labarai Kalaman TY Danjuma da na sauran Shugabannin Arewa

Kalaman TY Danjuma da na sauran Shugabannin Arewa

0
Kalaman TY Danjuma da na sauran Shugabannin Arewa

Daga Yasir Ramadan Gwale

An ruwaito Janar TY danjuma mai ritaya yana kiran al’ummarsa da  su tashi domin kare kansu daga hare haren da ake kai musu. Idan ba’a manta ba jihar Taraba, inda nan ce jihar da Danjuma ya fito ta sha fama da yawan hare hare, daga na ramuwar gayya sai na ‘yan ta’adda da suke shiga kauye su kashe mutanan kauyen baki daya, irin wannan hare hare da ake zargin Fulani da ‘yan kabilar Bachama da kuma kabilar Mambila sun sha kaiwa juna wadannan hare hare babu ji babu gani.

A irin wadannan kashe kashe da ake yi a jihar Taraba, babu babba babu yaro, babu mace babu namiji, duk lokacin da aka tashi yin irin wannan kisa zaka samu an nuna rashin Imani da rashin tausayi a cikinsa, kaga jariri da bai san komai ba, an yanka shi ko an cire kansa, haka nan tsofaffi da basa iya yin komai suma an sha samun gawarwakinsu an yi musu kisa na gilla da nuna rashin mutunci da rashin imani, mutumin da ba zai iya yin komai ba, hatta kansa ba zai iya amfanawa ba, amma an bishi inda yake kwance an kashe shi, saboda kawai ana kiyayya ko adawa da kabilarsa.

Irin wadannan kashe kashe na rashin imani da rashin sanin ya kamata, dole ya harzuka duk wani mai imani. Abin ban haushi da takaici shi ne yadda hukumomin tsaro basa iya yin komai kan irin wadannan kashe kashe, walau dakatar da shi ko kuma hukunta duk wanda aka samu da hannu wajen aikata irin wannan ta’addanci, da yawan wadan da suke jagorantar irin wadannan kashe kashe an sansu a yankunansu, amma anyi shiru kamar sun fi karfin doka, sai dai bayan an gama kai hare hare an kashe mutane an kone dukiyoyinsu sannan ne ma watakila hukumomin tsaro zasu san abinda yake faruwa, sannan a fara batun tura jami’an tsaro a wajen bayan anyi duk abinda za’ai an gama.

Irin wadannan kisan kiyashi da dangoginsu da suka auku a jihar Taraba, kuma hukumomi a matakin tarayya dana jiha suka gaza yin abinda ya dace domin kawo karshen wannan zubar da jini da kuma hasarar dukiya mai dumbin yawa. Domin shi wannan kisa na rashin imani a duk lokacin da aka yi shi zaka samu bayan an kashe mutanen sannan kuma za’a je a kone musu dukiyoyi, an bankawa gidajensu wuta duk abinda suka mallaka ya kone, sannan kuma a je idan Fulani ne a kore musu shanu sannan a kashe na kashewa, duk wadannan abubuwa ne da dole su harzuka mutane.

Na tabbatar faruwar irin wadannan kashe kashe akai akai ba tare da hukumomi sun dauki wani kwakkwaran mataki na tsayar da abin ba, da kuma hukunta wadan da aka samu da hannu, ya sanya Janar TY Danjuma mai ritaya irin wancan furuci da yace mutane su tashi tsaye domin kare kansu tunda yake hukumomi sun gaza kare al’ummar da suke Shugabanta.

Tun bayan wancan kalamai na TY Danjuma, mutane da yawa suka dinga yin Allah wadai da TY Danjuma da irin maganganun da yayi, a cewar wasu da dama musamman a shafukan sada zumunta na intanet, bai kamata ace babban mutum kamar TY Danjuma a same shi da irin wadannan maganganu ba. Da yawan mutane sun fadi maganganu marasa dadi akansa dangane da wannan furuci da yayi.

Zance na gaskiya idan zamu yiwa kanmu adalci, TY Danjuma ba shi ne ya fara irin wadannan kalamai ba. A baya zamanin Gwamnatin Goodluck Jonathan lokacin da aka kai harin Masallacin Juma’ah na cikin Birnin Kano, Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II da kansa ya fito yace jama’a su fito domin su kare kansu, a cewarsa Gwamnati ta gaza sauke nauyin da ke kanta na wajibi na kula da rayuka da dukiyoyin al’umma, a lokacin da Mai Martaba Sarkin Kano yayi irin wwadancan kalamai, ya zama gwarzo a wajenmu, mun yi ta kambama shi da nuna cewar ai irinsa muke so a matsayin Shugabanni masu kishi.

Irin kalaman da TY Danjuma yayi a yanzu irinsu ne dai Sarkin Kano yayi a zamanin Gwamnatin Jonathan lokacin da aka kai hari masallacin Juma’ah na cikin birnin Kano. Kuma shi kansa TY Danjuma din ya taba yin irin wannan kalami zamanin gwamnatin Jonathan lokacin da ake yawan kai hare haren Boko Haram.

Haka nan kuma, Shugaban kasa Muhammadu Buhari lokacin yana dan adawa da gwamnatin Jonathan shima yayi irin wadannan kalamai na nuna cewar mutane su tashi tsaye domin baiwa kansu kariya, jaridu da dama sun ruwaito Shugaba Buhari yana irin wadannan kalamai na TY Danjuma, haka zalika Malam Nasiru el-Rufai, yana daya daga cikin wadan da sautinsu ya dinga amo zamanin Gwamnatin Jonathan, babu abinda bai ce ba kan irin kashe kashen da ake yi, yayi kira ga jama’a da su kare kansu saboda yana adawa da gwamnatin Jonathan ta wancan lokacin.

To amma me ye ya sanya mutane suka yi saurin mancewa da kalaman Shugabannin Arewa wadan da suka yiwa Goodluck Jonathan adawa yayin da suke jin cewar ana kaiwa al’ummarsu hare haren kare dangi? Sai yanzu da aka samu TY Danjuma yayi irin wadacan kalamai sannan ya zama abin laifi? Wato dole mu ajiye abinda ake kira da turanci ‘Sentiment’ mu fuskanci gaskiya, mu fuskanci matsalolin kasarnan da idon basira domin ganin mun kawo karshensu.

Shugaba kowanne iri ne a matakin Gwamnatin Tsakiya ya sani shi ba Shugabane na kabilarsa ko yarensa ko yankinsa ba. Dole mu sani kuma dole Shugabanninmu su yarda cewar su Shugabanni ne na al’ummar Najeriya baki daya ba wasu tsirarun mutane ba, yin mulkin na Adalci da baiwa kowanne mai hakki hakkinsa da kuma sanya komai inda ya dace, wannan shi  ne zai sanya ‘yan kasa su zauna lafiya da juna, ba’a danne wani dan fifita wani ba.

Babu wani abu da zai zaunar da wannan kasar lafiya face Adalci a Shugabanci. Idan Shugabanni suka zama adalai to zasu samu cikakkiyar biyayya da kuma kiyaye dokokin hukuma, duk wanda yayi laifi komai girmansa komai mukaminsa komai kudinsa a hukunta shi, ba tare da la’akari da kabilarsa da yankinsa ba.

To amma muna gani jama’a suna gani, ga wanda yayi musu laifi an same shi dumu dumu da aikata laifi, amma kuma yana yawonsa lafiya lau ba abinda ya same shi, saboda kawai ya san wasu ko ya san wanda suka san wasu, mutum yayi dukkan shegantakarsa ya kwana lafiya saboda dan kabilarsu ko yankinsu ne ke kan mulki, dole Gwamnati ta kuduri aniyar babu sani babu sabo, duk wanda yayi ayi masa.

A baya muna ganin yadda Mujahid Asari Dokubu ya dinga kalamai na rashin albarka, amma shiru aka ki daukan mataki akansa saboda yana da uwa a gindin murhu, jami’an tsaro suna kallonsa suka ki daukar mataki akansa, ya dinga cin karensa babu babbaka, to ire iren wadannan abubuwan da suke aukuwa sune matsalolin kasarnan da idan ba’a warwaresu ba, to za’a jima ana fama da matsalolin tsaro, babu yadda za’a ace wasu mutane sun zama shalele suyi duk abinda suke so ga ‘yan kabilar da ba tasu ba babu kuma abinda zai faru, hukumomin tsaro suna ji suna ganni amma zasu yi kamar basu gani ba, saboda basa son su batawa ‘yan siyasa don kada wani abu da suke son samu ya kubuce musu.

To amma Shugabanni su sani ko sun yarda ko basu yarda ba, Allah yana ganinsu, kuma duk wanda aka zalinta sai Allah ya bi masa hakkinsa, ba daidai bane Shugabanni su dinga wasarairai da rayukan al’umma, ana ji ana gani wasu tsiraru suna kasha al’umma babu ji babu gani, amma anki daukar matakin day a dace a kansu, wannan sam ba daidai bane, kuma dole a dawo daga rakiyar irin wannan shakulatun bangaro da ake yi da rayuwar al’umma, duk wanda yayi hukunci yah au kansa ko waye shi kuma ko daga ina ya fito, to irin haka zai sanya mutane su samu nutsuwar cewar za’a yi musu adalci akan duk abinda ya shafe su. Allah ya bamu lafiya da zaman lafiya.