Home Labarai Gobara ta lashe Sakatariyar hukumar zabe ta jihar Kaduna

Gobara ta lashe Sakatariyar hukumar zabe ta jihar Kaduna

0
Gobara ta lashe Sakatariyar hukumar zabe ta jihar Kaduna

Wata mummunar gobara a ranar Asabar, ta lashe sakatariyar hukumar zabe ta jihar Kaduna (KADSIECOM), kwanaki kadan kafin gudanar da zaben kananan hukumomin jihar baki daya.

An sanya za’a gudanar da zaben kanananhukumomin jihar 23 da mazabun kansiloli 255 a ranar 12 ga watan Mayu mai kamawa.

Wani da abin ya faru a kan idonsa, ya tabbatar da da kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, cewar, wata gagarumar gobara ce ta kama ginin sakatariyar hukumar da misalin 11:24 na safiyar Asabar, a ginin hukumar dake kan titin Sakkwato a jihar Kaduna.

Ibrahim Musa, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya, yace yaga bakin hayaki ya turnuke sararin samaniya, wanda ake iya hango shi daga ne, yace ofisoshin dake samanbene a ginin hukumar ne suka kama da wuta.

Har ya zuwa wannan lokacin ba’a bayyana musabbabin tashin wannan gobara ba, anga jami’an hukumar kwana kwana na kokarin kashe wannan gobara.

Hukumar dai ta bayyana cewar ta sayo na’urar tantance masu jefa kuri’ah har guda dubu shida, wanda duk sun kone kurmus.

Har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto Shugabar hukumar Saratu Dikko da ta iso wajen da gobarar ke ci, taki yadda ta yi magana da ‘yan jarida.

(NAN)