Home Labarai Kano: Hisbah ta kama mawakin Tijjaniyya dake zagin Allah

Kano: Hisbah ta kama mawakin Tijjaniyya dake zagin Allah

0
Kano: Hisbah ta kama mawakin Tijjaniyya dake zagin Allah

Rundunar dakarun hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wani mawakin darikar Tijjaniyya da yayi wata waka yana zagin Allah da Manzonsa.

Shugaban hukumar Malam Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana hakan ne a wajen wa’azin kasa da kungiyar Jama’atu Izalatul Bid’ah Waikamatus Sunnah mai hedikwata a Jos ta shirya ranar Asabarda daddare a kano.

Da yake jawabin a wajen wa’azin, Sheikh Daurawa yace “hukumarsa ta ci nasarar cafke wannan mawaki, ina kwamandan yace tuni suka gurfanar da mawakin domin girbar abinda ya shuka”.

Hukamar Hisbar dai ta bayyana hakan ne a shafinta na facebook.