Home Labarai EFCC ta cafke sabon Babban Darektan First Bank Holdings

EFCC ta cafke sabon Babban Darektan First Bank Holdings

0
EFCC ta cafke sabon Babban Darektan First Bank Holdings

 

Rahotanni sun baiyana cewa Hukumar Yaƙi da Cin-hanci da Rashawa, EFCC ta kama da tuhumar sabon Babban Darektan First Bank Holdings, Nnamdi Okonkwo.

Jaridar Punch ta rawaito cewa tuhumar da a ke yinwa Okonkwo na da nasaba da rawar da a ke zargin ya taka wajen aika wasu kuɗaɗe har dala miliyan 150 da su ke da alaƙa tsohuwar Ministar Man-fetur, Diezani Alison-Madueke.

Jaridar ta rawaito cewa EFCC na zargin Alison-Madueke da sace dala miliyan 150 daga asusun Kamfanin Man-fetur na Nijeriya ta kuma ajiye su a wasu bankuna guda uku a cikin ƙasar.

Idan za a iya tunawa, a watan Janairun 2017 ne EFCC ta baiyana cewa Okonkwo, wanda shine tsohon Babban Darektan bankin Fidelity, ya taimakawa Alison-Madueke ta fitar da maƙudan kuɗaɗen, inda ta ajiye dala miliyan a wajen tsohon Babban Darekta ɓangaren kula da asusun jama’a na First Bank, Dauda Lawan da niyar yin basaja don ka da a gano asalin fitar kuɗaɗen.

A 6 ga watan Janairu ne EFCC ɗin ta nemi kotu, a ƙarƙashin mai shari’a Muslim Hassan ta nemi umarnin ko yi do ta sahale mata ta karɓe kuɗin ta danƙawa gwamnatin tarayya na wucin-gadi.