
Shahararren mawaƙin nan ɗan Nijeriya, Davido ya nemi masoyansa da su tallafa masa da naira miliyan 80 domin ya biya kuɗin ɗauko sabuwar motar da ya saya a filin jirgin sama.
Davido ɗin dai ya wallafa roƙon ma sa ne a shafinsa na twitter, inda ya ce ya sai motar ne kan zunzurutun kuɗi $330,000, daidai da N136,125,000.
A yanzu haka Davido ɗin ya baiyana cewa an tara masa Naira miliyan 114, inda ya baiyana ƙwarin gwiwarsa cewa zai samu kuɗin da zai ɗauki motar kirar Rolls Royce, wadda mota ce ta alfarma.