
Dakarun ƴan sanda a motoci huɗu ɗauke da makamai sun tsare harabar shalkwatar sakatariyar APC da ke a Blantyre Street, Abuja.
Jaridar Punch ta rawaito cewa a yau ne a ka ƴan sandan inda jami’an DSS ke mara musu baya, sun dira a harabar ne domin daƙile wani yunƙuri na karya doka da oda.
Jaridar ta rawaito cewa an kawo jami’an tsaron ne domin hana yin zanga-zanga wacce fusatattun ƴan jam’iya ke shirin yi sakamakon zaɓukan shugabannin mazaɓa, ƙananan hukumomi da na jihohi.