
Hukumar Yaƙi da Cin-hanci da Rashawa, EFCC, ta musanta rahotannin da a ke yaɗawa cewa ta samu rigunan mama na miliyoyin dala a kadarorin da ƙwace na tsohuwar Ministar Man-fetur, Diezani Alison-Madueke.
Shugaban hukumar, Abdulrasheed Bawa ne ya baiyana hakan a wata hira da a ka yi da shi ta kafar talabijin ta TVC ranar Laraba, inda ya ce labarin rigar mama ta gwal da aka ce akwai ta a cikin kayan na ƙanzon kurege ne.
“Babu wani abu mai kama da rigar mama ta gwal, maganar ‘yan kafafen sada zumunta ce,” in ji shi.
“Zan iya faɗa muku a kyauta saboda ni ne jagoran wannan binciken. Ban san da ita ba. Idan da akwai ta ya kamata a ce na sani. Ya kamata na sani saboda ni na jagoranci binciken da sauransu.”
Ana zargin Diezani wadda ta fice daga Najeriya a 2015 da satar kuɗin da suka kai dala biliyan biyu da rabi daga asusun gwamnatin ƙasa a lokacin da take minista, kodayake ta musanta zargin.
A watan Mayu ne Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa ya faɗa wa Majalisar Wakilai cewa darajar sarkoki da awarwaro da sauran kayan ƙawa da aka ƙwace daga wurin Diezani ta kai naira biliyan 14.
A watan Oktoba gwamnatin tarayya ta lissafa wasu kadarorinta da ta ƙwace waɗanda suka haɗa da gidaje a Banana Island da ke Ikoyi ta Jihar Legas.
Daily Nigerian Hausa