Home Labarai Tubabbun ƴan Boko Haram sun yi zan-zanga, sun faffasa kayan gwamnati a Maiduguri

Tubabbun ƴan Boko Haram sun yi zan-zanga, sun faffasa kayan gwamnati a Maiduguri

0
Tubabbun ƴan Boko Haram sun yi zan-zanga, sun faffasa kayan gwamnati a Maiduguri

 

Tubabbun ƴan Boko Haram da a ka killace su a sansanoni daban-daban a Maiduguri ta Jijar Borno sun koka da cewa an zaunar da su ba tare da sun san makomarsu ba.

Jaridar Punch ta rawaito cewa tubabbun mayaƙan na zanga-zanga ne a kan an jibge su wata da watanni.

Jaridar ta rawaito cewa tubabbun mayaƙan da a ka killace su a sansanin da ke cikin Maiduguri ne su ke yin zanga-zangar.

Majiyoyi daga ɓangaren jami’an tsaron da ke gadin sansanonin sun baiyana cewa tubabbun ƴan ta’addan na ƙorafi ne a kan cewa gwamnati ba ta maida su cikin mutanen gari ba, ba ta kuma basu abin yi ba ta kawai jibge su ba abinda su ke yi sai zaman banza.

Jaridar Punch ɗin ta kara da cewa tubabbun ƴan ta’addan na ƙorafi cewa an bar su a sanasani har tsawon watanni huɗu ba tare da sun haɗu da matansu ba, inda wasu na da mata biyu, wasu uku wasu ma huɗu.

Jaridar ta kara da cewa a yayin zanga-zangar, ƴan ta’addan sun faffasa wasu kayaiyakin gwamnati da kuma wasu gine-gine a cikin sansanonin.

Jaridar ta kuma baiyana cewa tuni wasu daga cikin tubabbun ƴan ta’addan su ka tsere zuwa cikin gari inndansu ka haɗu da ƴan uwansu da danginsu.

Amma kuma, da ta ke maida martani game da rahoton, Kwamishiniyar mata ta Jihar Borno, Hajiya Zuwaira Gambo, ta musanta rahoton, inda ta ce labarin ƙanzon kurege ne kawai.

Ta baiyana cewa duk abinda a ke faɗa ya faru a wannan sansani na cikin gari wanda shine sansanin alhazan jihar, ƙarya ne bai faru ba.

“Na ɗan yi tafiya bana gari. Amma da na dawo na kuma je sabanin yau, tubabbun mayaƙan ma murna su ka riƙa yi da su ka gan su na ta cewa mama, mama, mama.

“Ba su yi wata zanga-zanga ba ballantana ma su lalata kayan gwamnati,” in ji ta.