Home Ilimi SUBEB za ta sa almajirai 10,500 a makaranta a Kaduna

SUBEB za ta sa almajirai 10,500 a makaranta a Kaduna

0
SUBEB za ta sa almajirai 10,500 a makaranta a Kaduna

 

Hukumar Ilimin Bai-ɗaya, SUBEB ta Jihar Kaduna ta haɗa gwiwa da ma su ruwa da tsaki a kan kai almajirai ƴan asalin jihar guda 10,500 waɗan da a ka dawo da su jihar.

Shugaban SUBEB ɗin, Tijjani Abdullahi je ya baiyana hakan a wani taro na masu ruwa da tsaki a ranar Alhamis a Kaduna.

Ya ce jahohin da su ka maida almajiran da a ka dawo musu da su makarantu to za a basu lada mai tsoka.

Bugu-da-ƙari, SUBEB, a ƙarƙashin wani tsari na samar da ilimi a matakin farko ga kowanne yaro, BESDA, na shirin mayar da yara mata 24,000 da maza 16,500 marasa ƙarfi makaranta a ƙananan hukumomi 14 na jihar.