Home Labarai Ƴan sanda sun cafke farfesan da ya yi lalata da ƙaramar yarinya

Ƴan sanda sun cafke farfesan da ya yi lalata da ƙaramar yarinya

0
Ƴan sanda sun cafke farfesan da ya yi lalata da ƙaramar yarinya

 

 

Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Ebonyi ta tabbatar da cafke Felix Anyaegbunam sakamakon zargin yin lalata da ƙaramar yarinya.

Shi dai Anyaegbunam Farfesa ne a fannin Geophysics a jami’ar Alex Ekwueme Federal University, Ndufu-Alike, (AE-FUNAI), ƙaramar hukumar Ikwo a Ebonyi.

Rundunar ta ce farfesan ya daɗe ya na lalata da yarinyar ƴar shekara 13 kuma ƴar aiki gidansa ce wacce a ka haife ta a karamar hukumar Ezza ta arewa.

Kakakin rundunar, DSP Loveth Odah, ya shaidawa manema labarai ta kafar WhatsApp cewa wanda a ke zargin ya na hannun ƴan sanda.

“Kwamishinan Ƴan Sanda, Aliyu Garba ya bada umarnin binciken ƙwaƙwaf a kan lamarin yayin da a ke tsimayen sakamakon gwaje-gwajen lafiya da likitoci su ka yi mata,” in ji Kakakin.

A nashi ɓangaren, Shugaban Ƙungiya mai rajin yaƙi da cin zarafin mata da ƙananan yara, GBV, Faithvin Nwancho wacce ta kai ƙarar farfesan ta yi alla-wadai da laifin.

Ta yi zargin cewa a kulli-yomin sai farfesan ya yi lalata da yarinyar ƴar shekara 13, in da ta ce “a kowacce safiya sai ya yi lalata da ita.”

“Da Allah Ya yi dubunsa za ta cika, shine maƙota su ka fuskanci abin da ya ke faruwa. Sai su ka zo su ka sanar da mu. Shine mu ka yi maza mu ka fadawa ƴan sanda su kuma su ka cafke shi.

Nwancho ta yi kira ga ƴan sanda da su tabbatar da an bi wa yarinyar haƙƙinta, inda ta yi zargin cewa farfesan ya taɓa ɗirkawa wata yarinya ciki har lamarin ya sanya ta ajiye karatunta.