Home Ilimi Gwamnatin Yobe za ta cire kashi 10 na albashin ma’aikata na Nuwamba don bunƙasa ilimi

Gwamnatin Yobe za ta cire kashi 10 na albashin ma’aikata na Nuwamba don bunƙasa ilimi

0
Gwamnatin Yobe za ta cire kashi 10 na albashin ma’aikata na Nuwamba don bunƙasa ilimi

 

 

Gwamnatin Jihar Yobe ta ce za ta cire kashi 10 cikin 100 na albashin ma’aikata na watan Nuwamba a matsayin gudunmawarsu wajen gyara harkar ilimi a jihar.

Kwamishinan Harkokin Cikin gida, Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Muhammad Lamin ne ya baiyana hakan a taron manema labarai da ya yi a Damaturu a jiya Litinin.

Lamin ya baiyana cewa gwamnatin ta ɗauki matakin ne domin a haɗa hannu wajen farfaɗo da harkar ilimi wacce ta lalace sakamakon aiyukan ƴan ta’adda sama da shekara 10 a jihar.

Ya nuna cewa aiyukan ƴan ta’addan da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa ya gurgunta rayuwar al’umma, harkokin ilimi da gine-gine a jihar.

A ranar 9 ga watan Nuwamba ne dai Gwamnan Jihar Yobe ɗin Mai Mala Buni ya kafa kwamitin tara tallafin ilimi na mutum 25 da nufin tara kuɗaɗe domin farfaɗo da ilimi a jihar.