
Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Lai Mohamed ya sa ƙafa ya shure rahoton da kwamitin bincike kan #EndSARS ya kaiwa gwamnatin Legas a kan zargin kisa da a ka ce an yi a ƙofar Lekki.
Ministan ya siffanta rahoton da cewa tatsuniyar gizo ce kawai.
A rahoton kwamitin na mutum tara ya yi zargin cewa an kashe a ƙalla mutane 9 a ƙofar Lekki ɗin lokacin da ƴan sanda su ka dira wajen domin korar ma su zanga-zanga a ranar 20 ga watan Oktoba, 2020.
Yayin da ya ke ganawa da manema labarai a Abuja a yau Talata, Mohamed sai babu wata shaida game da baturuwan da rahoton ya ƙunsa.
Ministan ya yi mamakin cewa yadda kwamitin ya tattara ƙorafe-ƙorafen ƴan ƙasa su ka yi ya kuma kaiwa gwamnati.
Ya ce “kwamitin binciken bai yi bayani a kan iyalan waɗanda a ka ce an kashe , wai sai cewa a kai wai su na tsoron bada bayanai.
“To ai ko akuya ta na da wanda ya ke kula da ita kuma ya je ya nemo ta idan ya ga ba ta dawo gida ba, ballantana ɗan adam.
“Ina iyalan waɗanda a ka ce an kashe ɗin a kofar Lekki? Idan har kwamitin binciken ya bada ƙudurin a biya su diyya, to ina sunayen su da kuma adreshinsu ya ke? Wa zai karɓi diyyar bayan har yanzu ba wanda ya nuna kansa har kawo yau?”
Mohamed ya ƙarƙare da cewa ba za a dogara da gaskiyar rahoton ba domin cike ya ke da batutuwa ma su kokwanto.