
Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Kano ta ce ta gano gawar mutane biyu, mace da namiji a wata mota, ƙirar Siyana a kan titin zuwa Katsina a jihar.
A wata sanarwa da Kakakin Rundunar Ƴan Sanda ta jihar, Abdullahi Kiyawa ya fitar a jiya Alhamis, rundunar ta ce ta gano mamatan, wanda ta baiyana sunayensu da Steven Ayika da kuma Chiamaka Emmanuel, dukkanin su ƴan unguwar Jaba da ke Ƙaramar Hukumar Fagge, a kwance a kujerar baya na motar.
Kiyawa ya ƙara da cewa rundunar ta ƙarɓi rahoto cewa an ga wasu mutane biyu a kwance a cikin mota ba sa motsi, inda tuni jami’anta su ka garzaya wajen.
Kiyawa ya ce “A ranar 23/11/2021 da misalin karfe 4:50 na safe, mun samu rahoton cewa an ga wata mota a kan hanyar Katsina, dake karamar hukumar Fagge ta jihar Kano dauke da mutane biyu a ciki, namiji da mace a kwance ba sa motsi.
“Bayan samun rahoton, Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya umurci tawagar ƴan sanda ɓangaren bincike da su garzaya gurin da lamarin ya faru.
“Nan take tawagar ta garzaya gurin da lamarin ya faru. Nan take a ka kwashe gawawwakin, inda a ka garzaya da su asibitin kwararru na Murtala Mohammed Kano. A nan ne wani likitan ya tabbatar da cewa sun rasu.
“Yanzu dai a na ci gaba da bincike,” in ji Kiyawa.