
Sarki Salman na Saudi Arebiya ya bada umarnin da a bar masallata, waɗanda ba masu Ummara ba su yi ɗawafi a filin da Ka’aba ta ke da ga ƙasa daga ranar Alhamis.
Wannan na ƙunshe ne a sanarwar da Kakakin Babban Ofishin Kula da Harkokin Masallatan Harami Guda Biyu, Haider ya fitar.
Ya ce da ga yanzu an ware filin jikin ka’aba domin waɗanda ba alhazan Ummara ba su yi ɗawafi, inda ofishin ya ware musu lokuta uku domin yin ɗawafin.
“Babban Ofishin, da haɗin gwiwar sauran ma’aikatu a masallacin Harami sun kammala shirye-shiryen tarbar masu yin ibada a masallacin da kuma yin ɗawafi a lokuta guda uku.
“Lokutan su ne 7:00 zuwa 10:00 na safe, 9:00 zuwa 11:59 na dare, sai kuma 12:00 na dare zuwa 3:00 na dare,” in ji shi.
Heider ya ƙara da cewa duk wata hidima da ta kamata za a yiwa masallatan, da su ka haɗa da ba da zam-zam, feshin maganin kashe ƙananan cututtuka, da kuma shigarwa da fitar da masallatan.
Ya kuma ƙara da cewa an tanadi duk wani tsare-tsare da zai bayar da damar filin ya ɗauki masallata komai yawansu.
Daily Nigerian Hausa