
Daga Hassan Y.A. Malik
Rundunar ‘yan sandan yaki da fashi da makami ta SARS sun kara tsare sanatan da ke wakiltar mazabar Kogi ta yamma sanata Dino Melaye a safiyar yau Talata.
‘Yan sandan sun tsare Sanata Dino Melaye ne a ofishin hukumarsu dake kallon tsohon babban bankin Nijeriya, akan babban titin Area 1 a birnin Abuja.
Ofishin da jami’an SARS suka tsare Dino, an tanade shi ne domin ajiye masu laifi da ke nuna taurin kai bayan an kama su da laifin sata, kisan kai, sirri da sauran ayyukan laifi a Abuja
Idan masu karatu basu manta ba, a safiyyar jiya Litinin ne aka fara kama Sanatan a filin jirgin saman Abuja a hanyarsa na zuwa kasar Morocco kamar yadda shi sanatan da kansa ya bayyana a shafinsa na Twitter
Daga baya aka sake shi a jiya da rana inda a yanzu haka an kuma kama shi.