Home Siyasa Zaɓen Shugabannin APC: Kwamiti zai fara sulhunta Ganduje da Shekarau

Zaɓen Shugabannin APC: Kwamiti zai fara sulhunta Ganduje da Shekarau

0
Zaɓen Shugabannin APC: Kwamiti zai fara sulhunta Ganduje da Shekarau

 

 

Kwamitin sulhu da jam’iyar APC ta kafa ya ce zai fara aiki ne ta jihar Kano da ga ranar Litinin.

A kwanan nan ne dai rikici ya ɓarke a APC a Jihar Kano, inda jam’iyar ta rabe biyu tsakanin ɓangaren Gwamna mai ci, Abdullahi Ganduje da tsohon gwamna kuma Sanata mai ci, Ibrahim Shekarau.

Bayan an yi zaɓen shugabannin jam’iya na jiha, kowa, a tsakanin Abdullahi Abbas na tsagin Ganduje da Ummaru Ɗan-Zago na ɓangaren Shekarau na iƙirarin cewa shi ne sahihin shugaban jam’iya a jihar.

Bayan haka, a kwanannan ne dai uwar jam’iyar APC ta ƙasa ta kafa kwamiti a ƙarƙashin jagorancin Sanata Abdullahi Adamu kuma tsohon gwamnan Jihar Nasarawa.

Da ya ke ganawa da manema labarai a Abuja, Sanata Adamu ya ce kwamitin zai fara aikin sulhu ne ta Kano.

A ganawar tasa da manema labarai, Adamu ya baiwa ƴan Nijeriya tabbacin yin adalci ga fusatattun ƴan jam’iyar da su ka gabatar da ƙorafin su ga uwar jam’iyar domin samun zaman lafiya mai ɗorewa.

Sanata Adamu ya ce manufar ita ce a tabbatar da an sulhunta duk waɗanda su ka samu saɓani kafin babban taron jam’iyar na ƙasa ya zo nan ba da daɗewa ba.

Shugaban Kwamitin ya ƙara da cewa, shugabannin jam’iyyar sun damu matuƙa da matsalolin da su ka dabaibaye ta, musamman a matakan jihohi, in da ya bada tabbacin za su samar da zaman lafiya tsakanin ƴan jam’iyar ta kowane hali.

Sanata Abdullahi Adamu ya ce kwamitin ya yanke shawarar fara aikinsa a jihar Kano a ranar litinin ɗin nan mai zuwa domin warware .atsalar da jam’iyar APC ke fuskanta don ya zama masomin nasarar kwamitin.

 

Daily Nigerian Hausa