
…sun riƙe guda uku sai an kai musu babura 3
Rundunar ƴan sanda ta Jihar Kaduna ta tabbatar da sakin 10 da ga cikin 13 na ma’aikatan ƙaramar hukumar Zariya da ke Kaduna.
Mohammed Jalige, Kakakin eundunar, shine ya shaidawa manema labarai a Zariya a yau Lahadi, inda ya ce tun a jiya Asabar a ka sake su kuma an ci gaba da ƙoƙarin sakin sauran ma’aikata guda uku.
Sai dai kuma Jalige, mai muƙamin ASP, ya ƙi ya faɗi ko an biya kuɗin fansa kafin sakin ma’aikatan.
Amma kuma wata majiya ranta nemi a sakaya sunanta ta shaidawa Kamfanin Daillancin Labarai, NAN cewa ma’aikatan sai da su ka biya naira miliyan 40 sannan a ka sako su.
Majiyar ta ƙara da cewa ƴan uwan waɗan da a ka yi garkuwa da su ɗin nen su ka haɗa kuɗaɗen.
Ta ƙara da cewa kuma masu garkuwa da mutane ɗin ba su saki sauran mutum uku ba saboda sharuɗɗan da su ka gindaya bayan an biya miliyan 40 ɗin nan shine cewa za su rike mutum uku har sai an sai musu baburura guda uku sabo fil.