
Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’a, JAMB ta baiyana cewa da ga yanzu ita ce za ta riƙa karɓar Naira 700 da a ke biya a cibiyoyin zanawa da yin rijistar jarrabawar, CBT daga shekarar 2022.
JAMB ta ce ta ɗauki wannan hukunci ne sabo da ta daƙile almundahana.
A mujallarta da ta ke wallafawa mako-mako, wacce ta saki a ranar Litinin a Abuja, JAMB ta baiyana cewa za ta riƙa karɓar N700 ɗin a lokacin yin rijista, inda da ha bisani sai ta rarrabawa masu CBT ɗin.
Mujallar ta yi bayanin cewa bayan an kammala Jarrabawar, za ta rarraba kuɗaɗen da ta tara na rijista ga duk cibiyoyin, inda ta ce “za mu karɓi lambar asusun kowacce cibiya sai mu aika mata da iya adadin kuɗin da kowacce cibiya ta cancanta ta karɓa.”
“Wannan matakin an ɗauke shi ne a co gaba da yunƙurin tsaftace harkokin Jarrabawar bayan da a ka samu wasu bayanai na badaƙalar kuɗaɗe,”
Daily Nigerian Hausa