
Daga Hassan Y.A. Malik
Wani manomi mai shekaru 35 ya kashe kansa ta hanyar rataya bayan da ya kashe matarsa mai shekaru 32.
Manomin da aka bayyana sunansa ya fusata ne bayan da ya dawo daga gona, amma a maimakon ya samu mai dakinsa mai suna Ama Baduwa ta shirya masa abincin da ya fi so, wato fufu (sakwarar rogo), kawai sai ya tarar da ita tana sharar bacci.
Lamarin dai ya faru ne a unguwar Awugyekrom da ke kusa da Adansi Fumso duk a yankin Ashanti ta Ghana a safiyar jiya Litinin
Ibrahim Abu, wanda kawu ne ga manomin ya bayyana cewa sun tsinci gawar dan dan uwan nasa ne na reto a jikin wata bishiya bayan da ya rataye kansa.
A cewar Ibrahim Abu, Emmanuel ya yi wa matarsa dan karan duka kafin ya sa adda ya yi mata raunin da har sai da ta fadi kasa a mace. Wata majiyar ta ce dama dai Emmanuel na zargin mai dakinsa da bin maza, wannan ne ma ya sanya fushin nasa ya yi tsanani.
Shugaban rundunar ‘yan sandan yankin, Adansi Fomena, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya kara da cewa tuni dai ‘yan sanda suka debi gawarwakin ma’auratan suka ajiyesu a mutuwaren sabon asibitin gwamnati na Edubuasi, yayin da ‘yan sanda ke ci gaba da gabatar da bincike.