Home Labarai Buhari ya miƙa ta’aziyar rasuwar Sarkin Bai Kano, Mukhtar Adnan

Buhari ya miƙa ta’aziyar rasuwar Sarkin Bai Kano, Mukhtar Adnan

0
Buhari ya miƙa ta’aziyar rasuwar Sarkin Bai Kano, Mukhtar Adnan

 

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya miƙa ta’aziyar rasuwar Sarkin Ban Kano, Mukhtar Adnan.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mataimakin shugaban ƙasar kan kafafen yaɗa labarai, Garba Shehu sanya fitar a ranar Juma’a a Abuja.

Buhari ya baiyana cewa rasuwar Sarkin Bai, mai shekara 95 kuma mai naɗa sarki mafi tsufa a tarihin Kano ta zama cewa babban bango ne ya faɗi, duba da yadda ya tara tarihi a harkokin aiki.

Sarkin Bai wani babba ne a wanda ya bada gudunmawa sosai a siyasa da kuma al’adun mu.

“Tarihin da Adnan ya kafa na kasancewa a masarauta tsawon shekaru 63 sannan ya zama bulaliyar majalisa a jamhuriya ta ɗaya inda hakan ya maida shi wani ginshiƙi ja tarihin kafuwar Nijeriya,”

Buhari ya ƙara da cewa ɗaya da ga cikin manyan kyawawan halayen marigayin shine nagartaraa da kowa ya san shi da ita.