
A wani yanayi na ramuwar gaiya, jami’an Ma’aikatar Ƙasa da Safiyo ta Jihar Kano sun sake kulle ofishin babban lauyan nan, Nureini Jimoh, wanda ya samu gagarumar nasara a kan Jam’iyar APC, ɓangaren Gwamna Abdullahi Ganduje har kotu ta rushe shugabacin Abdullahi Abbas a jihar.
Daily Nigerian Hausa ta rawiato cewa kwana ɗaya da samun nasarar a kotu, wacce ta tabbatar da Ahmadu Ɗanzago na tsagin Sanata Shekarau a matsayin shugaban jam’iyar APC a Kano, kwatsam sai gani a kai jami’an gwamnati da ƴan sanda sun garƙame baki ɗaya ginin da ofishin lauyan ya ke.
Amma, bayan ƙorafe-ƙorafe da ga al’umma, da kuma ƙungiyar lauyoyi, sai gwamnatin ta buɗe ofishin.
Sai dai kuma, a wani yanayi na shege-ka-fasa, kwatsam sai wayar garin Jumaa a ka yi a ka ga gwamnatin ta sake kulle wannan waje.
Wata majiya da take da alaƙa da lamarin, cikin ɓacin rai, ta shaidawa jaridar DAILY NIGERIAN, cewa “yau an wayi gari da ganin ci gaban yaƙi da ƴan adawa da gwamnatin Kano ta ke yi, inda ta sake garƙame wannan gini da ofishin lauyan Shekarau ke ciki.”
“Duk garin nan ofishin nan ne kawai a ke yiwa haka. Tsakar dare su ka zo su ka kulle ginin. Wannan abin kunya ne ga gwamnatin Kano,” in ji majiyar.
Sai dai kuma, a ranar Alhamis, Ma’aikatar Ƙasa da Safiyo ɗin ta ɓara, inda ta ce kullewar gaba ɗaya ginin ta shafa, ba wai ofishin lauyan shi kaɗai ba.
Kakakin ma’aikatar, Murtala Umar ya yi ƙarin haske da cewa gidan mai ɗauke da sunan Isyaka Rabi’u & Sons, mai lamba C14/C16 da ke kan titin Murtala Mohammed, an kai masa takardar tuni kan ya biya haraji.
“Tun a ranar 14 ga Satumba kwamiti daga ma’aikatar nan ya kai musu takardar tunatarwa. Bayan nan a ka sake kai musu ta gargaɗi da su zo da su biya kuɗaɗen da a ke bin su tun daga 2016 zuwa 2021.
“Ba wai iya nan kaɗai mu ka kulle ba, mun rufe gidaje sun kai 30 a gurare da dama a garin nan.
“Kuma ma gidan da a ka kulle a titin Murtala Mohammed an kulle sakamakon kunne uwar shegu da su ka yi da tunatarwar da mu ka yi musu.
“Shi Nurein Jimoh haya yanke a wannan gida da mu ka kulle. Mu samuwar mu mai gidan, ba dan haya ba,” in ji shi.
A na ci gaba da ganin bi-ta-da-ƙulli da halin nuna isa a kan ƴan adawa a jihar nan, inda a ke kina ofisoshin waɗan da ba tafiyar su ɗaya da gwamnatin ba.